Yadda masu zanga-zanga suka fito a birnin Sanaa na Yemen domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa. Hoto/Reuters

Dubban mutane suka fito suna tattaki domin nuna goyon bayansu ga kungiyoyin Falasdinawa bayan wani harin ba-zata da suka kai kan wasu wurare da Yahudawa suke zaune ba kan ka'ida ba, lamarin da ya jawo asarar daruruwan rayuka.

Kungiyar Hamas, wadda ke mulkar Gaza da aka mamaye, ta bayyana cewa abin da ya sa suka kai wannan harin shi ne karin hare-haren da ake kai wa Falasdinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma a Birnin Kudus wadanda duka wurare ne da Isra'ilar ta mamaye.

Haka kuma Hamas din ta ce daga cikin dalilan wadannan hare-hare har da ci gaba da rike wasu Falasdinawa a gidan yarin Isra'ila.

Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama inda sama da Falasdinawa 230 suka rasu sa'annan aka bukaci mazauna Gaza da su yi gaggawar barin gidajensu.

Yemen

Dubban mutane a kasar Yemen suka fito a Sanaa babban birnin kasar domin nuna goyon bayansu ga kungiyar Hamas wadda ke yaki da Isra'ila.

Dubban mutane sun fito a Yemen domin nuna goyon baya ga Hamas. Hoto/Reuters

Turkiyya

A birnin Santambul da Ankara da wasu birane na Turkiyya, mutane da dama sun fito inda suke nuna goyon baya ga Falasdinawa da ke Gaza da sauran sassan duniya a daidai lokacin da ake yaki tsakanin Falasdinawa da kuma dakarun Isra'ila

A Diyarbakir, wasu daga cikin Turkawa sun nuna goyon bayansu ga Falasdinawa. Hoto/AFP
Wasu mata a yayin da suke fadin suna goyon bayan Falasdinawa a yayin wani tattaki da aka gudanar a birnin Santambul. Hoto/Others

Iraki

'Yan kasar Iraki sun yi tattaki a Bagadaza babban birnin kasar domin nuna goyon baya ga Falasdinawa. Haka kuma masu tattakin sun rinka kona tutocin Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

'Yan kasar Iraki sun kona tutar Isra'ila a lokacin da suke tattakin goyon bayan Falasdinawa. Hoto/AFP

Iran

'Yan kasar Iran sun taru a Tehran babban birnin kasar, inda suke dauke da tutocin Falasdinu da kuma hotunan kwamandan sojojin juyin-juya-hali na Iran wanda aka kashe wato Qasem Soleimani - wanda ake zargin Isra'ila ce ta kashe shi.

'Yan kasar Iran sun halarci wani gangami a Tehran domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa. Hoto/AFP

Maroko

A Maroko, mutane sun daga tutocin Falasdinawa da kuma alluna wadanda suka rubuta "babu sulhu da 'yan Isra'ila" a lokacin da ake tattaki domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.

Mutane da dama sun gudanar da zanga-zanga dauke da tutocin Falasdinu inda suke nuna goyon baya a garesu, Hoto/AA 

Lebanon

A Beirut babbar birnin Lebanon, mutane da dama sun dauki tutocin Falasdinawa wadanda suka rubuta "turjiya ita ce kadai hanyar karbo Masallacin Aqsa" domin nuna goyon baya ga Falasdinawa.

 Mutane rike da tutoci domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa, Hoto/Reuters

Jordan

'Yan kasar Jordan da dama sun taru a kusa da ofishin jakadancin Isra'ila da ke Amman babban birnin kasar domin nuna goyon baya ga Falasdinawa inda suke rike da tutoci.

'Yan kasar Jordan sun taru a lokacin zanga-zanga domin nuna goyon baya ga Falasdinawan da ke Gaza kusa da ofishin jakadancin Isra'ila da ke Amman. Hoto/Reuters
TRT World