Sai dai babu wani mamba Musulmi a ministocinsa duk da ana ganin hakan zai iya sauyawa nan gaba. / Hoto: AP

Narendra Modi ya soma wa'adinsa na uku a matsayin Firaministan India, inda manyan ƙawayensa suke kawo sauyi kan manufar jam'iyyarsa mai rinjaye, suna dagewa kan cewa shirye-shiryensu na kula da Musulmai za su ci gaba da tabbatar da jin daɗin tsiraru mafi girma na al 'ummar ƙasar.

Modi ya yi rantsuwar kama aiki a ranar Lahadin da ta gabata a matsayin shugaban gwamnati mai mambobi 72 wacce ta haɗa da mambobi biyu kowannen su daga Telegu Desam Party (TDP) da Janata Dal-United (JDU) - waɗanda goyon bayansu ke da matukar muhimmanci ga jam'iyyar 'yan kishin ƙasa ta Modi mabiya addinin Hindu Bharatiya Janata Party (BJP).

Duk da cewa har yanzu ba a rarraba ofisoshi ba, an fahimci cewa BJP za ta ci gaba da riƙe manyan ma'aikatun cikin gida da kuɗi da tsaro, kamar yadda Modi ya samu hanyar da zai ci gaba da bai wa 'yan jam'iyyarsa damar juya gwamnatin haɗakarsa a halin yanzu.

Sai dai babu wani mamba Musulmi a ministocin Modi, duk da cewa akwai yiwuwar hakan ya sauya nan gaba.

A lokacin da aka sanar da zaɓen India a ranar 4 ga watan Yuni, Modi da jam'iyyarsa ta BJP sun shiga matuƙar ruɗani. A karon farko tun 2014, jam'iyyar ba ta samu adadin ƙuri'un da ake buƙata ba domin kafa gwamnati.

A majalisar dokokin ƙasar mai mambobi 543, jam'iyya ko kuma haɗakar jam'iyyu na buƙatar rinjayen kujeru 272 domin kafa gwamnati. A 2014, BJP ta samu kujeru 282, wanda suka samu ci gaba a 2019 da 303. Sai dai a bana, BJP ɗin ta samu ƙuri'u 240.

Sai dai wannan na nufin tun bayan da Modi ya hau mulki a 2014 bayan samun rinjaye, wannan ne karon garko da ya dogara kan haɗakar jam'iyyu domin komawa kan mulki a karo na uku.

TDP da kuma JD(U) sun kasance tamakar masu naɗin sarki sakamakon su ke da kujeru mafi rinjaye bayan BJP a rukunin jam'iyyunsu, waɗanda ake kira National Democratic Alliance (NDA) waɗanda ke da kujeru 16 da 12.

Wannan ne ya sa wani babban ɗan jarida wanda ya jima yana bayar da rahoto game da BJP fiye da shekara 20, ya yi bayani kan cewa TDP da JD(U) duka an ba su kujerun ministoci biyu. A gwamnatin Modi ta baya, ƙawayen haɗaka suna samun kujera ɗaya ce kawai, a matsayin tukuici.

Walwalar al'ummar Musulmi

Bayan gudanar da yaƙin neman zaɓe mai zafi wanda ya mayar da hankali kan sukar Musulmai, waɗanda su ne kaso 14 cikin 100 na masu jefa ƙuri'a a ƙasar, Jam'iyyar BJP a halin yanzu ta samu kanta a tsaka mai wuya domin tana hannin ƙawayenta waɗanda ke tausaya wa Musulman.

Manyan 'yan Jam'iyyar BJP, daga ciki har da firaminista, a lokacin yaƙin neman zaɓe sun ta iƙirarin cewa idan aka zaɓi 'yan adawa, za su bai wa Musulmi a ƙasar ƙarin iko, wanda hakan wani tsari ne da alama BJP ɗin take matuƙar adawa da shi.

A gabashin jihar Bihar, alal misali, Modi ya bayyana cewa " 'Yan adawa na son ƙwace SC da ST da OBC daga wurinku zuwa ga masu jihadi. A game da haka, suna son sauya kundin tsarin mulki, sai dai domin kada haka ya tabbata, akwai buƙatar ku samu gwamnatin mai ƙarfi a tsakiya.

Sai dai Nara Lokesh, wanda ɗan majalisa ne a Jam'iyyar TDP kuma ɗa ga Chandrababu Naidu wanda jagora ne a jam'iyyar, ya bayyana cewa jam'iyyarsu za ta ci gaba da bai wa Musulmai gurbi a jiharsu ta Andhra Pradesh.

"A zahiri take cewa 'yan tsiraru na ci gaba da shan wahala kuma suna da mafi ƙarancin samun kuɗin shiga. A matsayinmu na gwamnati alhakinmu ne fitar da su daga ƙangin talauci. Don haka duk shawarar da zan yanke ba don jin dadi ba ne, amma don fitar da su daga kangin talauci,” kamar yadda ya shaida wa tashar talabijin ta Indiya NDTV.

Haka kuma a kwanakin baya an yi ta samun fargaba a duniya dangane da yadda ake musguna wa Musulmai marasa rinjaye a Indiya a ƙarƙashin mulkin Modi, kamar yadda mai magana da yawun JD(U) na ƙasa KC Tyagi ya bayyana.

Mai magana da yawun TDP Jyothsna Tirunagari ya shaida wa TRT World cewa sun ɗauki matsaya kan ba za su kawo cikas kan batun gurbin Musulmai ba kuma idan sun fuskanci wata matsala "ko bambancin ra'ayi," za su "tattauna da kuma neman mafita."

Haka shi ma wani mai magana da yawun JD(U) Satya Prakash Mishra ya bayyana cewa jam'iyyarsu ba ta goyi bayan siyasar ɓangaranci ba, haka kuma ƙawancen NDA an yi shi ne domin "ci gaban duk wasu sassa na al'umma".

Bambancin ra'ayoyin abokan haɗin gwiwar ba asara ce ga mutane. Tsohuwar 'yar jarida Arati Jerath ta ce dole ne BJP ta yi watsi da kalaman rarrabuwar kawuna idan Modi na son gudanar da haɗin gwiwa cikin lumana.

"Idan shi (Modi) yana son ya nuna alamun zaman lafiya na gwamnati, ba zai bar muryoyin rikice-rikice ba," kamar yadda ta fada wa TRT World yayin da ta kara da cewa BJP za ta kasance da "matsakaicin ra'ayi" a yanzu.

"Saƙon masu jefa kuri'a shi ne cewa su ma sun gaji da siyasar Hindu da Musulmai... Ina jin siyasar Hindu-Musulmai ba ta da sauran muhimmanci," kamar yadda ta yi ƙarin bayani.

Akwai yiwuwar BJP tana sane da irin "sauye-sauyen" da ya kamata ta yi.

Lokacin da Atal (Bihari Vajpayee) ya zama Firaiminista shi ma, akwai jam'iyyu da yawa a cikin haɗin gwiwar kuma dole ne mu sassuata kan wasu batutuwanmu kamar (wajen ibada na) Ram Mandir. Dole ne mu ɗan sassauta a wasu lokuta, dole ne su ɗan sassauta a wasu lokuta, "in ji babban jagoran BJP Prabhat Jha a tattaunawarsa da TRT World.

Ƙarfin BJP

Ko da yake rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa TDP da JDU na sane da ƙarfinsu kuma sun bukaci kujerun ministoci shida, amma sai dai su haƙuar da mukama biyu-biyu da aka ba su.

"Akwai yiwuwar ta wani ɓangaren Modi ya yi ƙoƙarin shawo kansu. Watakila ana ganin ya ce zai biya musu buƙatunsu," kamar yadda Jerath ta shaida wa TRT World.

Babbar 'yar jaridar na ganin Modi da na hannun damnasa Amit Shah, "sun yi gagarumin ƙoƙari wajen kafa haɗaka," kuma dukansu babu wanda ke son "nuna gazawa".

"Kuma hakan ya dogara ne kan ofishin da aka ba su (aka ba ƙawayen). Abin da ya fi muhimmanci shi ne ofishi, ba wai adadin kujerun da aka ba su ba," kamar yadda ta shaida wa TRT World.

Shugabannin TDP da JD(U), Chandrababu Naidu da Nitish Kumar, dukkansu ’yan siyasa ne na zamanin ƙawancen da suka san yadda za su yi yarjeniya. Sai dai Jerath ya ce abin da zai yi musu cikas wajen yarjejenyar shi ne har yanzu kujerun jam'iyyun adawa 230 ne kawai.

"Ina tsammanin a halin yanzu, batu ne na ina za su tafi su je in sun fice daga haɗakar Modi. Ba wani adadinsu na ƙaruwa ba ne a wani bangaren, ko kuma za su je su kafa gwamnati a ɗaya bangaren,” inji ta.

Haka kuma, Mishra ta shaida wa TRT World cewa ba su yi wata yarjejeniya ba. "Abin da aka ba mu, mun amince," kamar yadda ya bayyana.

Sai dai a wa'adinsa na uku, akwai buƙatar gwamnatin ta Modi ta faranta wa ƙarin ƙawaye, idan aka yi la'akari da girman majalisar ministocin da aka rantsar da su tare da Modi.

"Idan aka gwada Modi a karon farko da karo na biyu, a wannan karon an fi samun abokan haɗaka da ƙarancin 'yan jam'iyyar BJP," a cewar babban ɗan jaridar da ya nemi a sakaya sunasa.

TRT World