1552 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa 201 a Gaza a kwana daya
Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta fitar da sanarwa a ranar Asabar inda ta ce akalla Falasdinawa 201 aka kashe haka kuma an raunata mutum 368 a Gaza a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Tun daga 7 ga watan Oktoba, adadin Falasdinawa da Isra’ila ta kashe ya kai 20,258, inda adadin wadanda suka samu rauni ya kai 53,688, kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.
1455 GMT — Kiristocin Gaza sun ce bana za su yi Kirisimeti cikin 'bakin ciki'
Wani malamin addinin Kirista na Falasdinu ya koka kan cewa bikin za a yi bikin Kirisimetin bana cikin “bakin ciki”.
A wata tattaunawa da aka yi da shi, Mitri Raheb ya shaida cewa a rayuwarsa bai taba fuskanatar bala’i irin wannan ba.
Ya bayyana cewa zuwa yanzu an kashe kashi uku cikin 100 na Kiristocin da ke zaune a Gaza.
1403 GMT — Wasu mazauna Gaza na sayar da kayayyakinsu don su siya abinci: WHO
Mazauna Gaza na fuskantar barazanar yunwa inda suke sayar da kayayyakinsu domin neman abinci, kamar yadda Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya bayyana.
“Akwai yunwa, kuma karancin abinci na karuwa a Gaza,” kamar yadda Tedros Adhanom Ghebreyesus ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Hudu cikin biyar na gidaje a arewacin Gaza da kuma rabin mutanen da suka rasa muhallansu a kudanci na shafe dare da rana ba tare da sun ci abinci ba, in ji Ghebreyesus.
1314 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 76 'yan gida daya a Gaza
Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya yi sanadin mutuwar mutum 76 wadanda suka fito dangi guda, kamar yadda jami’an da ke aikin ceto suka tabbatar.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan cewa babu wani wuri mai aminci da mutum zai iya tsira a Gaza.
Harin wanda aka kai a gidan iyalan Mughrabi, ya yi sanadin mutuwar masu gidan 16, sai kuma mata da yara da dama.
Daga cikin wadanda suka rasu har da Issam al Mughrabi, wani babban ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya, inda aka kashe shi da matarsa da ‘ya’yansa biyar.