Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum a Gaza waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: AA

Aƙalla Falasɗinawa 25 Isra’ila ta kashe a Gaza daga ciki har da ma’aikata uku na ƙungiyar samar da abinci ta World Central Kitchen da kuma jikkata gommai a daidai lokacin da Isra’ila ke ƙara zafafa hare-hare a Zirin Gaza.

Majiyoyin kiwon lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Falasɗinawa bakwai daga ciki har da ma’aikatan World Central Kitchen Isra’ilar ta kashe a wani hari ta sama wanda aka kai kan wata mota da ke ɗauke da farar hula a Khan Younis.

A cikin birnin na Gaza kuwa, mutum bakwai Isra’ilar ta kashe a wani hari da ta kai wani gida da ke unguwar Al-Rimal, kamar yadda hukumar kare fararen hula ta Falasɗinawa ta tabbatar.

An kashe wasu ƙarin Falasdinawa 10 a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani gida a unguwar Shujaiya da ke gabashin birnin Gaza, kamar yadda wata majiyar lafiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

0500 GMT — Wakilan Hamas sun nufi birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa kan yiwuwar tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda wani jami'i na ƙungiyar ta Hamas ya bayyana.

Sai dai duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta tayar da bam a unguwar Sheikh Radwan da ke cikin birnin Gaza inda ta kashe Falasɗinawa 10.

Wani jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari kan wani gida mallakar iyalan as-Sardi da ke unguwar inda farar hula 10 suka rasu, wasu kuma suka jikkata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Isra'ila WAFA ya tabbatar.

0030 GMT — An gudanar da zanga-zanga 105 a biranen Morocco 48 domin nuna goyon baya ga Gaza

An gudanar da zanga-zanga 105 a ranar Juma'a a biranen Moroko 48 don yin tir da hare-haren Isra'ila da nuna goyon baya ga Gaza.

Dubban jama'a ne suka taru a wuraren da jama'a ke yin zanga-zangar domin amsa kiraye-kirayen kungiyoyin fararen hula, ciki har da hukumar kare muradun al'ummar kasar Morocco.

Masu zanga-zangar sun nuna bacin rai da nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu

TRT Afrika da abokan hulda