Sojojin Isra’ila sun saɓa ƙa’idar yarjejeniyar tsagaita wuta da Lebanon sau bakwai, ciki har da harbi a ƙauyukan dake kudancin Lebanon, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Lebanon NNA ya bayyana.
Saɓa yarjejeniyar ta fi faruwa ne a gundumar Marjayoun ƙarƙashin yankin Nabatieh da kuma gundumar Tyre.
Wata tankar yaƙin Isra’ila ta harba bam wani gida a yankin Tel Nahas kusa da Burj Al-Moulouk, inda mai gidan ya tsallake rijiya da baya, wanda bai jima da shiga gida ba, a cewar NNA.
Sojojin sun kuma harba bama-bamai garuruwan Markaba da Talloussa da Odaisseh da Taybeh da kuma Houla, sannan sun tura tankokin yaƙi hudu zuwa yammacin Khiyam.
A Khiyam, an ba da rahoton cewa sojojin Isra’ila sun buɗe wuta kan wasu mutane da suke tafiya wajen jana’iza.
Haka kuma a wani wajen, motocin rushe gini na Isra’ila sun tunɓuke bishiyoyin zaitun sun kuma share gonaki a yankin Abbara da ke Kfarkela.
Tawagar Hamas za ta yi tattaunawar tsagaita wuta a Masar: Hukumomi
Wakilan Hamas za su je birnin Alƙahira na Masar a ranar Asabar domin tattaunawa kan yiwuwar tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda wani jami’i a ƙungiyar gwagwarmayar ta Falasɗinawa ya shaida wa kamfanin dilllancin labarai na AFP.
“Wata tawagar Hamas za ta je Alkahira gobe domin gudanar da tattaunawa da dama tare da jami’an Masar don tattauna batutuwa kan tsagaita wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni a Zirin Gaza,” a cewar jami’in, wanda bai so a bayyana sunansa ba, saboda girman batun.