Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un daga hannun dama a yayin da yake kallon wani wasa tare da Ministan Tsaron Rasha Andrei Belousov daga hannun hagu a Pyongyang. / Hoto: AFP

Ministan Tsaron Rasha Andrei Belousov ya gana da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un, inda suka amince da karfafa hadin gwiwar soji tsakanin kasashen biyu, in ji kafar yada labaran gwamnatin Pyongyang a ranar Asabar.

Amurka da Koriya ta Kudu na zargin Koriya ta Arewa wadda ke da makamin nukiliya da tura sojoji fiye da 10,000 don taimaka wa Rasha yaki da Ukraine, inda masana ke cewa Kim na da muradin samun ci gaban fasahar kere-kere, da kwarewar yaki da sojojinsa, a maimakon haka.

Kim, wanda ya gana da Belousov a ranar Juma'a, ya soki matakin baya-bayan nan da manyan kasashen Yammacin duniya suka ɗauka na barin Kiev ta kai hari a cikin Rasha da makamansu, yana mai cewa hakan ya zama "amfani da soji kai tsaye a wannan rikici", a cewar KCNA.

"Aiki ne na 'yancin kare kai ga Rasha ta dauki kwakkwaran mataki don hukunta sojojin abokan gaba yadda ya kamata,” kamar yadda Kim ya bayyana.

A ranar Asabar KCNA ta bayyana cewa, ziyarar Belousov za ta taimaka matuka gaya wajen karfafa karfin tsaron kasashen biyu da... ƙara kaimi, hadin gwiwa da ci gaban dangantakar da ke tsakanin sojojin ƙasashen biyu.

Belousov, a cikin wata sanarwa, ya nuna godiya ga yauƙaƙa danƙon zumuncin da kasashen biyu ke yi, tare da yaba wa Koriya ta Arewa "bisa manufofinta na ƙasashen waje”.

TRT World