Harin da Isra'ila ta kai a Rafah da ke kudancin Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. An kai gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa Asibitin Nasser, ciki har da ‘ya’yan wata mahaifiya wadda ke cike da baƙin ciki, wanda daya daga cikinsu ya ba ta kodar sa wata guda daya gabata. / Hoto: AA

0945 GMT — Kusan Falasɗinawa 100 suka rasu a wani mummunan “kisan kiyashi” da Isra’ila ta aikata a cikin kwana guda a Gaza, kamar yadda Hukumar Kare Farar Hula ta Gaza ta sanar.

Mutum bakwai ciki har da yara biyu na daga cikin waɗanda Isra’ilar ta kashe a Gaza, in ji wasu majiyoyi na kiwon lafiya.

Wata majiya ta ɓangaren kiwon lafiya ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa, an kashe Falasdinawa hudu a harin da Isra'ila ta kai kan wasu fararen hula a sansanin 'yan gudun hijira na Shaboura da ke kudancin birnin Rafah.

Yara biyu ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama suka jikkata a lokacin da wani jirgin sama mai saukar ungulu na Isra'ila ya afka wa wani tanti da ya kasance mafaka a Al-Mawasi da ke Khan Younis, in ji majiyar.

A tsakiyar Gaza, wani Bafalasdine daya ya mutu a wani harin da Isra’ila ta kai kan wani gida da ke yankin Al-Mufti da ke arewacin sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, in ji ma’aikatan jinya.

0450 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kakkaɓo wasu makamai da aka harba daga Yemen kafin su isa cikin Isra'ila.

Tun da farko rundunar sojin ta Isra'ila ta kaɗa jiniya a yankuna da dama na tsakiyar ƙasar sakamakon makamai da aka harba mata daga Yemen.

Mayaƙan ƙungiyar Houthi sun harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa Isra'ila babu ƙaƙƙautawa sakamakon abin da suka bayyana a matsayin goyon bayan Falasɗinawa, tun da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza a 2023.

2041 GMT — Ƙungiyar WCK ta dakatar da aiki a Gaza bayan mummunan harin Isra'il a kan ma'aikatanta

Ƙungiyar samar da abinci ta World Central Kitchen (WCK) ta dakatar da aiki a Gaza sakamakon harin da Isra'ila ta kai ta sama kan motar dake ɗauke da ma'aikatanta, wanda ya kashe mutum biyar.

A cikin wata sanarwa a X, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan lamarin, ta kuma tabbatar da cewa har yanzu tana tattara bayanai.

"Muna cikin jimamin bayyana cewa hare-haren jiragen sama a Gaza sun faɗa kan motar dake ɗauke da ma'aikatan agaji na ƙungiyar World Central Kitchen," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A cikin wata sanarwa a X, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan lamarin, ta kuma tabbatar da cewa har yanzu tana tattara bayanai./ Hoto: Reuters

2114 GMT — Majalisar Faransa ta goyi bayan soke taro da Rima Hassan za ta gabatar

Ƙarin labarai 👇

Wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ce tana la'akari da ɗaukaka ƙara dangane da ƙalubalantar soke jawabin da aka shirya gudanarwa a jami'ar Sciences Po University.

Majalisar ta yanke hukuncin cewa soke taron da hukumomin makarantar suka yi bai wani take haƙƙin faɗin albarkacin baki na a-zo-a-gani ba, abin da ke nan ya sa ta soke hukuncin da kotun baya ta yanke ta kuma tabbatar da soke gabatar da jawabin.

Majalisar Ƙasa ta Faransa ta tabbatar da wani hukunci da ya soke wani jawabi a wata jami'a a birnin Paris da aka shirya Rima Hassan za ta gabatar, wacce 'yar majalisar Tarayyar Turai ce kuma 'yar asalin Falasɗinu daga jam'iyyar Unyielding France (LFI).

Ba wannan ne karon farko da aka soke jawabin da Rima Hassan za ta gabatar ba.

TRT World