Sojojin Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: Reuters / Photo: AA

Lahadi, 3 ga watan Nuwamba, 2024

1210 GMT –– Akalla karin Falasdinawa 27 ne Isra’ila ta kashe a hare-haren da ta kai a Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 43,341, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 102,105 sun jikkata a harin da ake ci gaba da kaiwa.

"Sojojin Isra'ila sun kashe mutum 27 tare da jikkata wasu 86 a kisan gilla da aka yi wa iyalai hudu a cikin sa'o'i 24 da suka wuce," in ji ma'aikatar.

0943 GMT — Gurneti ta halaka wani sojin Isra'ila a arewacin Gaza

Rundunar Sojin Isra’ila ta bayyana cewa wani sojanta ya mutu a arewacin Gaza bayan gurneti ta fashe a hannunsa.

Kafar watsa labarai ta Channel 13 ta Isra’ila ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar haka kuma ana gudanar da bincike domin gano dalilin da ya jawo fashewar gurnetin.

Mutuwar sojin na Isra’ila ta sa adadin sojin ƙasar da suka mutu tun bayan soma yaƙin Gaza zuwa 780, kamar yadda ƙididdigar sojin ƙasar ta nuna. Daga cikin waɗannan, mutum 368 sun mutu ne a yayin da suke kai farmaki ta ƙasa a cikin Gaza.

0058 GMT — Isra'ila ta kai hari a wani gida a Gaza, ta kashe Falasɗinawa da dama — rahotanni

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama tare da jikkata gommai a harin bam da dakarunta suka kai da sanyin safiyar ranar Lahadi a wani gida da ke yankin Tal al-Hawa na kudu maso yammacin Birnin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa, Wafa, ya ambato majiyoyi da dama a yankin suna cewa Isra'ila ta kashe mutane da yawa da jikkata gomma bayan ta rurga bama-bamai a gidan Abu Al-Auf da ke Tal al-Hawa, inda aka rika yi wa ma'aikatan agaji kiran gaggawa domin su kai ɗauki a gidan.

Tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara ne Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza, inda ta yi wa ɗaukacin yankin ƙawanya.

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 43,314, sannan an yi amanna dubbai na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai.

TRT World