Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza a kullum waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: Reuters

1332 GMT Akalla karin Falasdinawa 55 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila a zirin Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 43,314, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza a ranar Asabar.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 102,019 sun jikkata a harin da ake ci gaba da kaiwa.

"Sojojin Isra'ila sun kashe mutum 55 tare da jikkata wasu 192 a kisan kiyashi bakwai da suka yi kan wasu iyalai a cikin sa'o'i 24 da suka gabata," in ji ma'aikatar.

0927 GMT — Wani makamin roka da aka harba daga Lebanon ya jikkata mutum 19 a Isra'ila

Wani makamin roka da aka harba daga Lebanon ya jikkata mutum 19 a Isra’ila bayan makamin ya faɗa kan wani gini a garin Tira a ranar Asabar.

Sojojin Isra’ila sun bayar da rahoton ƙarar jiniya a yankunan Sharon da Dan a daidai lokacin da aka harba makaman roka uku daga Lebanon inda suka shiga sararin samaniyar Isra’ila.

Duk da cewa an yi ƙoƙarin daƙile makaman, akwai ɗaya daga cikin makaman da ya wuce inda ya faɗa a cikin Isra’ilar.

Rundunar sojin ta kuma ce an harba rokoki 10 daga kasar Lebanon zuwa yankunan Haifa Bay da Galili a arewacin Isra'ila. An daƙile wasu, yayin da wasu suka fadi a wuraren da babu gidaje.

0703 GMT — Akalla Falasdinawa 8 ne suka rasu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a arewaci da tsakiyar Gaza.

Majiyoyin lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Falasdinawa uku ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata lokacin da sojojin Isra'ila suka kai hari a unguwar Saftawi da ke arewacin birnin Gaza.

A gefe guda kuma, kanfanin dilancin labaren Falasdinawa WAFA ya bayar da rahoton cewa, harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai wa wani ginin mazaunin sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza ya kashe mutum biyar tare da jikkata wasu da dama.

TRT Afrika