Zaɓen shugaban ƙasa tsakanin Harris da Donald Trump a Amurka  ya ta’allaka ne kan sakamakon da aka samu a jihohi bakwai masu muhimmanci  / Hoto: AP

Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris da tsohon shugaban ƙasar Donald Trump suna ci gaba da matsa kaimi a fafatawar zaɓen ranar 5 ga watan Nuwamba, wanda ke zama zabe na kut-da-kut tsakanin 'yan takara a tarihin Amurka.

A muhimman jihohin da ke kan gaba a fafatawar ta 2024, ana iya cewa babu wata tazara sosai tsakanin abokan hamayyar biyu a zaben da za a gudanar kasa da sa'o'i 24.

A ƙarkashin ƙundin Tsarin Mulkin Amurka, manyan shugabannin baya da suka kafa ƙasar sun tabbatar da cewa kowace jiha daga cikin guda 50 da ake da su, suna da 'yancin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

A tsarin zaɓen Amurka , kowace jiha tana da adadin ƙuri'un “wakilain masu zabe,” bisa ga yawan al'ummarta. Yawancin jihohi suna da tsarin karba-karba wanda ke bai wa duk wanda ya lashe zaɓen fidda gwani damar samun kuri'u.

Kowane ɗan takara na buƙatar ƙuri’u 270 daga cikin 538 don samun nasara, akwai yiwuwar samun sakamakon zaɓen daga cikin ƴan tsirarun jihohin da ake kira "swings state'', wadanda suke da tarihin lashe zabe tsakanin 'yan takarar jam'iyyar Republican da Democrat.

A wannan shekara, za a fafata ne a muhimman jihohi guda bakwai, kuma kowanne daga cikinsu na da rawar da zai taka wajen samun nasara ko akasin haka:

Ga wasu ƙarin bayanai game da jihohin.

Pennsylvania ( ƙuri'un wakilan masu zaɓe 19 )

A baya Pennsylvania ta kasance jigo ga jam'iyyar Democrat, amma a yanzu ba ta da wani karfi kamar yadda aka santa a baya da zama ''Keystone State'' wato babbar jiha a taswirar fagen fama na zaɓe.

Ɗan takarar Republican Trump ya tsallake rijiya da baya a jihar mai mazauna mutum miliyan 13 da makin kuri'u 0.7 a shekarar 2016, yayin da Joe Biden ya yi nasara da kaso 1.2 cikin dari na kuri'un zaɓen shekarar 2020.

Georgia ( ƙuri'un wakilan masu zaɓe 16)

Jihar da ke yankin ƙudu maso Gabas ta kasance jiha da aka sanya wa ido sosai a ƙarshe wa'adin farko na mulkin Trump, sannan wadda ke cike da ce-ce-ku-ce.

Masu gabatar da kara a Georgia sun tuhumi Trump da yin katsalandan a cikin lamuran zaɓe bayan ya kira jami'an jihar yana mai buƙatar su ''nemo'' ƙuri'u masu yawa da za su hamɓarar da nasarar Biden a 2020.

Sai dai a wani yunkuri na karfafa wa Trump, an dakatar da shari'ar har sai bayan zaben.

Biden dai ya kasance ɗan jam'iyyar Democrat na farko da ya lashe zaɓe a jihar tun shekarar 1992. Sannan akwai yiwuwar sauye-sauyen alƙaluma a wannan karon su iya amfanar da Harris.

North Carolina (ƙuri'un wakilan masu zaɓe 16)

Jihar wadda take Kudu maso Gabas ta zaɓi jam'iyyar Democrat ne sau ɗaya kawai tun shekarar 1980, amma Harris ta yi imanin a wannan karon za ta iya samun nasara a jihar.

Yawan al'ummar jihar, waɗanda a yanzu suka haura mutum miliyan 10, suna ƙara ƙaruwa sannan mabambanta ne, yanayin da zai amfanar da 'yan jam'iyyar Democrat.

A cikin wani yanayi da ke ƙara dagula ƙalubalen da Trump ke ciki, wata badakalar da ta dabaibaye ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar Republican ta harzuka jami’an jam’iyyar, waɗanda ke fargabar hakan na iya kawo cikas ga damar nasarar Trump.

Kamar dai makwabciyarta Georgia, wani muhimmin abu da ka iya kasancewa shi ne yadda guguwar Helene, wacce ta yi barna a kwanakin baya-bayan nan a garuruwan da ke yammacin North Carolina, na iya yin tasiri a sakamakon zaɓen.

Michigan (ƙuri'un wakilan masu zaɓe 15)

Trump ya lashe Michigan, wadda ke zama tsohuwar tungar jam’iyyar Democrat a fafatawarsa da Hillary Clinton a shekarar 2016.

Biden ya kwace wannan nasarar a 2020, a wata haɗin gwiwar ƙungiyar ma'aikata da kuma al'ummar Baƙaƙen fata suka ba shi.

Sai dai a wannan karon, Harris na fuskantar barazanar rasa goyon bayan kuri'u 200,000 na al'ummar Larabawa-Amurkawa waɗanda suke sukar Biden - har da ita kanta - bisa ga yadda suke tafiyar da yakin Isra'ila a Gaza.

Arizona (ƙuri'un wakilai masu zaɓe 11)

Jihar Arizona wadda ake yi mata ƙirari da ''Grand Canyon'' tana daga cikin jihohin da aka fafata sosai a 2020, inda Biden ya yi nasara da ƙuri'u 10,457 kawai.

Trump na fatan manufofin shige da fice na gwamnatin Biden da Harris da ke cike da ƙalubale zai ba shi damar lashe jihar, wadda ke da iyaka da Mexico.

Harris ta kai ziyara iyakar Arizona a watan Satumba inda ta yi alƙawarin korar 'yan gudun hijira tare da farfado da yarjejeniyar dokar iyakoki tsakanin jam'iyyun biyu, wadda ta ce Trump ya "jikirta" bisa ga dalilansa na siyasa.

Wisconsin (ƙuri'un wakilai masu zaɓe 10)

Clinton ta yi rashin nasara a Wisconsin bayan ta ƙaurace wa jihar a yakin neman zabenta na 2016.

Kamar makwabciyarta Michigan, lamarin ya sauya bayan fafatawar Trump da Biden wanda ya samu kuri'u 23,000 da ya samar da gibi a kuri'u 21,000 na nasara 'yan Democrat.

Trump na kallon jihar a matsayin wacce za iya lashe zaɓe, kuma jam'iyyarsa ta gudanar da babban taronta na bazara a can.

Duk da cewa Trump ne ke kan gaba a karawarsa da Biden, Harris ta rike wuta wajen gangamin yakin zaɓenta.

Nevada (ƙuri'un wakilan masu zabe 6)

Jihar wacce ake kiranta da ''Silver state'' tana da mazauna har miliyan 3.1, ba ta goyi bayan wani ɗan takarar Republican ba tun shekara 2004.

Trump dai yana kan gaba a jihar fiye da Biden.

Amma a cikin makonnin da ta zama 'yar takarar Democrat, Harris - wadda ke tallata manufofinta kan tattalin arziƙin don taimakawa ƙananan 'yan kasuwa tare da dakile hauhawar farashi - ta kawar da wannan damar a jihar, wadda babban birninta Las Vegas ya cika ya batse da masana'antun da ke janyo baƙi.

TRT World
AFP