Duniya
Amurkawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa da ‘yan majalisun dokoki
Mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris da ɗan takarar jam’iyar Republican Donald Trump suna fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa inda yawancin ƙuri'un jin ra'ayin jama'a ke nuna tazarar kashi ɗaya zuwa uku cikin ɗari a tsakaninsu.Duniya
Zaben Amurka: Za a fafata a jihohi bakwai masu muhimmaci tsakanin Trump da Harris
Fafatawar da za a yi a ranar 5 ga watan Nuwamba tsakanin Harris da Donald Trump ta ta’allaka ne kan sakamakon da za a samu a jihohi bakwai masu muhimmanci, inda Trump da Harris ke ci gaba da matsa kaimi wajen samun ƙuri'u kwana ɗaya kafin ranar zaɓe.Duniya
'Waccan matar, ko wancan mutumin': Wane ne 'mai ɗan dama-dama a muguntar' da Paparoma yake magana a kai?
Gabanin zaben da aka shirya yi a ranar 5 ga watan Nuwamba, Fafaroma Francis ya bayyana 'yan takarar biyu a matsayin "mugwayen mutane" amma ya ƙara da cewa "dole ne ku zabi mai ɗan dama-damar".Duniya
Kamala Harris ta buƙaci kawo ƙarshen yaƙin Gaza, Trump na zarginta da ƙin jinin Isra'ila
A yayin muhawarar da aka shirya wa 'yan takarar shugabancin Amurka, tsohon shugaban ƙasar Donald Trump ya zargi Kamala Harris da "ƙin jinin Isra'ila,' inda ita kuma ta mayar da martani da cewa: 'Na shafe rayuwata ina goyon bayan Isra'ila'.Duniya
Musulman Amurka sun fi mabiya sauran addinai fuskantar wariya — Binciken Brookings
Kashi uku cikin ɗari ne kacal na Amurkawa suka yarda cewa Musulmai suna bayar da gudunmawa wajen ƙarfafa al'umma, inda magoya bayan jam'iyyun Democrat da Republican suke gani Musulmai ba sa tsinana wa ƙasar komai, a cewar binciken.
Shahararru
Mashahuran makaloli