Ƙyamar da ake yi wa Musulmai a Amurka ta yi matuƙar ƙaruwa, inda a halin yanzu aka fi tsanarsu fiye da yadda ake yi wa sauran addinai da ƙabilu, a cewar wata sabuwar ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da cibiyar Brookings Institution ta gudanar.
Binciken ya gano wani abu mai tayar da hankali game da kallon tsana da ake yi wa Musulmai da Musulunci a Amurka, inda ya kai matsayi daidai da abin da ya faru a lokacin mulkin Trump.
Abin da ya fi ɗaga hankali shi ne yadda aka samu ƙaruwar ƙyamar Musulmai a tsakanin magoya bayan jam'iyyar Democrat — mutanen da suka riƙa kare Musulmai daga wulaƙancin da Trump ya yi musu.
Binciken ya bankaɗo yadda ƙyamar Musulmai ta ginu a tsakanin Amurkawa. Amurkawan da suka yi karatu ne kawai suka fi sassaucin ra'ayi a kan Musulmai.
Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'ar da aka yi wa taken University of Maryland Critical Issues Poll (UMDCIP), wadda aka gudanar tsakanin 26 ga watan Yuli zuwa 1 ga watan Agusta kuma aka wallafa sakamakonta ranar Talata, ta mayar da hankali ne kan abu biyu: nazari kan sauye-sauyen ra'ayin Amurkawa game da Musulunci da Musulmai, da kuma nuna wariya ga ƙabilu da mabiya addinai daban-daban, ciki har da Yahudawa da Musulmai.
Abin ɓoye ya fito fili
Adadin Amurkawan da ba sa goyon bayan Musulmai su tsaya takara, ko da kuwa sun amince da aƙidun siyasarsu, ya ƙaru sosai, musamman a tsakanin 'yan jam'iyyar Republican.
Wannan ra'ayi ya yi daidai da daɗaɗɗen ra'ayin nan na ƙyamar 'yan takara da babu ruwansu da addini, abin da ke nuna tasirin addini a fagen siyasar ƙasar.
Binciken ya ce, "Kalaman da Shugaba Joe Biden yake yi, a lokacin da 'yan ƙasar suka mayar da hankali sosai kan yaƙin Isra'ila da Gaza, musamman kuma ra'ayin shugaban ƙasar, wanda wasu suka caccaka a matsayin nuna ƙyama ga Musulmai da Larabawa fararen-hula da aka kashe, sun nuna cewa yana wulaƙanta Larabawa da Musulmai."
Ƙuri'ar ra'ayin jama'ar ta nuna yadda ɗabi'un Amurkawa suke ƙara bayyana, inda ƙyamar Musulunci take kan gaba. A yayin da ake shirin gudanar da zaɓe a ƙasar, wannan bincike ya nuna cewa masu kaɗa ƙuri'a za su fi mayar da hankali kan ra'ayoyinsu na son kai, maimakon manufofin 'yan takara kafin su yi zaɓe.
"Ƙyamar da ake nuna wa Musulmai da Musulunci ta fi wacce ake yi wa Yahudawa da Yahudanci. Duk da yake a ƙuri'iar jin ra'ayin jama'a da muka gudanar a baya mun yi keɓantacciyar tambaya game da Musulunci da Musulmai, mun sake yin irin wannan tambaya a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya bayan nan ganin yadda ake samu ƙaruwar tsanar Yahudawa.
"Cikin waɗanda suka bayar da amsa, kashi 64 sun fi yabon Musulmai idan aka kwatanta da kashi 86 da suka fi yabon Yahudawa, sannan kashi 48 sun fi goyon bayan Musulunci, yayin da kashi 77 suka fi goyon bayan Yahudanci," a cewar binciken na Brookings.
An gudanar da binciken ne kan Amurkawa 1,510 baligai da kuma baƙaƙen-fata 202 da 'yan asalin ƙasashen da ke magana da harshen Sifaniya 200.