Dan jaridar nan dan kasar Iraki Muntazer al-Zaidi wanda ya ja hankalin duniya lokacin da ya jefi tsohon shugaban Amurka George W. Bush da takalmi yayin wani taron manem labarai, ya yi alkawarin bayar da “tukwici” ga duk wanda ya maimaita hakan kan shugaban Amurka Joe Biden.
"Zan bayar da tukwici ga duk dan jaridar da ya jefi shugaban Amurka [Joe Biden]," in ji Muntadhar al Zaidi a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.
Yana yin martani ne ga sakon wata mace da take neman inda yake a daidai lokacin da Biden ke ziyara a Isra’ila.
"Ina mutumin nan [al Zaidi] wanda ke dauke da takalmi? Muna bukatarsa a wannan lokaci fiye da koyaushe," in ji matashiyar mai amfani da shafin X, kuma Zaidi ya bayar da amsar cewa zai bayar da kyauta ga duk wanda ya yi namijin-kokari wajen wulla wa Biden takalmi.
A al’adar Larabawa, nuna wa mutum kasan takalmi wulakanci ne. Haka kuma jifan mutum da takalmi babban wulakanci ne.
Kasashen duniya musamman na Musulmai sun yi matukar harzuka ranar Laraba bayan Biden ya wanke Isra’ila daga zargin da ake yi mata na kai hari asibitin Al Ahli da ke Gaza inda ta kashe Falasdinawa fiye da 500 sannan ta jikkata da dama.
Biden ya kara harzuka jama'a bayan da ya yi takakkiya zuwa birnin Tel Aviv don bayyana goyon bayan Amurka ga Isra'ila, inda dubban mutane suka fantsama kan tituna don nuna kyama da Allah wadai kan hare-haren da Isra'ila take kai wa kan fararen-hula a Gaza.