Shugaban Amurka Joe Biden ya ce fashewar da ta ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 500 a asibitin Al Ahli Arab a Gaza ba hare-haren Isra'ila ta sama ne suka jawo.
"Daga abin da na gani, akwai alamun da ke nunawa cewa dayan bangaren ne suka kai harin, ba ku ba," in ji Biden a ranar Laraba yayin taron manema labarai tare da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
A fili yake yana goyon bayan ikirarin Isra'ila kan cewa kungiyar Islamic Jihad, wacce kungiyar Falasdinawa ce mai dauke da makamai, ita ce ta kai harin.
Duka kungiyoyin Islamic Jihad da Hamas sun yi watsi da ikirarin Isra'ila wacce ta ce wani makami mai linzami na Islamic Jihad ne ya kauce hanya ya fada wa asibitin da ya kashe mutum akalla 500.
"Akwai mutane da dama da ba su tabbatar ba, ya kamata mu shawo kan abubuwa da dama,"in ji shugaban kasar, wanda ya kai ziyara Isra'ila ana tsakiyar rikici da kungiyar Hamas.
Biden ya sha alwashin bai wa Isra'ila karin goyon baya yayin yaki da Falasdinawa, wanda rikicin ya koma yaki kwana 12 da suka wuce.
Ya dace a tabbatar da cewa Isra'ila ta "samu abin da take bukata ta kare kanta," in ji Biden, inda ya jaddada cewa Isra'ila tana da 'yancin kare kanta.
"Za mu tabbatar da cewa hakan ya tabbata kamar yadda kuka sani," kamar yadda ya shaida wa Netanyahu.
"Ya kuma kamata mu sani cewa Hamas ba wakiltar gaba daya Falasdinawa take yi ba, kungiyar tana jawo musu bala'i ne," in ji Biden.