Shugaban Amurka Joe Biden ya janye daga neman sake tsayawa takarar shugabancin kasar bayan wasu 'yan jam'iyyarsa ta Democrat sun matsa masa lamba don ya hakuri da takarar sakamakon rashin cikakkiyar lafiyar kwakwalwa.
A wani sako da Biden ya wallafa a shafin X, ya ce zai ci gaba da ayyukansa na shugaban Amurka kuma babban kwamandan tsaron kasar har karshen wa'adin mulkinsa na farko a watan Janairun 2025 kuma zai yi wa 'yan kasar jawabi a wannan makon.
"Abin alfahari ne a gare ni da na kasance shugaban Amurka. Ko da yake na yi niyyar sake tsayawa takara, na yi amanna zai fi kyau ga jam'iyyata da kuma kasar nan na janye daga takara sannan na mayar da hankali wurin aiwatar da ayyukana na shugaban kasa a ragowar wa'adina," in ji Biden.
A wani sako na daban da ya wallafa a shafin X, Biden ya goyi bayan Mataimakiyar Shugaban kasa Kamala Harris domin neman takarar shugaban Amurka a jam'iyyarsu ta Democrat.
"Matakin farko da na dauka bayan jam'iyya ta tsayar da ni takara a 2020 shi ne na dauki Kamala Harris a matsayin mataimakiyar shugaban kasa. Kuma wannan shi ne mataki mafi muhimmancin da na dauka," a cewarsa.
Ya kara da cewa, "A yau, ina bayar da dukkan goyon bayana ga Kamala domin zama 'yar takarar jam'iyyarmu a wannan shekarar. 'Yan Democrat — lokaci ya yi da za mu hada kai domin kayar da Trump."
Harris za ta kasance mace bakar-fata ta farko da za ta yi takarar shugaban Amurka a tarihi.
A martanin da ya mayar, Trump ya shaida wa CNN ranar Lahadi cewa yana ganin Harris za ta fi saurin kayarwa fiye da Biden a zaben da za a gudanar a watan Nuwamba.