Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya mika kansa ga mahukuntan gidan yarin Georgia inda ake tuhumarsa da lafin yunkurin murde zabe.
Ya kasance shugaban kasar na farko da aka dauki hoton fuskarsa a al'amarin da ya shafi aikata laifuka.
Trump, wanda ake zarginsa da hada baki da mutum 18 don murde zaben jihar na shekarar 2020, ya isa gidan yarin gundumar Fulton da ke jihar Atlanta ranar Alhamis.
Ya bar gidan yarin ne kusan minti 20 bayan ya isa.
Amma kafin a bayar da belin Mr Trump a kan $200,000, sai da aka dauki hotonsa da tsawonsa da kuma nauyinsa.
- Tsohon shugaban kasar ta Amurka ya yi gajeren jawabi ga 'yan jarida a yayin da yake kokarin shiga jirginsa.
- Ya ce: "Wannan mummunar rana ce ga Amurka da bai kamata irin haka ta faru ba".
- Wannan ne karo na hudu da ake zargin Donald Trump, wanda ke kan gaba a masu son yi wa jam'iyyar Republican takara a zaben 2024, da aikata manyan laifuka a wannan shekara.
- Sai dai ya sha cewa tuhume-tuhumen suna da alaka da siyasa.
TRT Afrika