Wata kotu a Georgia ta Amurka ta tuhumi tsohon shugaban kasar Donald Trump da laifin yunkurin murde zaben jihar duk da kayen da ya sha a zaben shugaban kasar na 2020.
Alkaliyar kotun yankin Fulton ta tuhumi Mr Trump da mutane 18 bisa zarge-zarge 41 da suka hada da yunkurin murde zaben kasar.
Wannan ne karo na hudu da aka tuhumi tsohon shugaban na Amurka da aikata manyan laifuka a wannan shekarar.
Sai dai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa.
A watan Fabrairun 2021 ne alkaliyar kotun yankin Fulton Mai Shari'a Fani Willis ta soma bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Mr Trump da makusantansa na yunkurin murde zabe.
Wasu daga cikin wadanda ake tuhuma su ne: lauyan Trump Rudy Giuliani, tsohon shugaban ma'aikatan Fadar White House Mark Meadows, tsohon lauyan Fadar White House John Eastman da kuma tsohon jami'in ma'aikatar shari'ar Amurka Jeffrey Clark.
"Trump da sauran wadanda ake tuhuma sun ki amincewa da shan kayen da Trump ya yi, kuma suna sane suka kitsa yunkurin murde sakamakon zaben don ya dace da muradun Trump," a cewar takardar tuhumar da ake yi musu wadda aka karanta a kotun.
Sai dai Mr Trump, wanda ke kan gaba a cikin masu son yi wa jam'iyyar Republican takara a zaben 2024, ya ce alkaliya Willis, wadda 'yar jam'iyyar Democrat ce, tana tuhumarsa ce domin cimma wasu muradu na "siyasa."
Mai shigar da kara ta jihar Georgia, wadda ta gurfanar da tsohon shugaban na Amurka da sauran wadanda ake tuhuma a kotu, ta ce tana so a soma yi musu shari'a "nan da wata shida masu zuwa."
Alkaliya Fani Willis ta ce ta bayar da izinin kama Trump da sauran mutanen da ake tuhuma kan zargin yunkurin murde zaben 2020 idan ba su mika kansu "salin-alin" ba ga hukumomi nan da ranar 25 ga watan Agusta.