Donald Trump ya ce tuhumar da ake yi masa na da alaka da siyasa./Hoto: Reuters

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya musanta tuhumar da wata kotun da ke Washington DC take yi masa ta yunkurin murde zaben shugaban kasar na 2020 bayan ya sha kaye.

Lokacin da ya gurfana a gaban kotun, ya yi magana cikin murya kasa-kasa inda ya bayyana cewa ba shi da laifi, sannan ya fadi sunansa da shekarunsa kuma ya ce babu wani tasirin miyagun kwayoyi a jikinsa.

Ya gurfana a gaban kotun ne kwana biyu bayan mai shigar da kara na Ma'aikatar Shari'ar Amurka Jack Smith ya zarge shi da aikata manyan laifuka hudu.

Trump, wanda ke kan gaba a cikin masu son tsayawa takarar shugaban Amurka a zaben 2024 a jam'iyyar Republican, na fuskantar tuhume-tuhumen da suka hada da hada baki wajen cin zarafin Amurka da kuma yunkurin hana majalisar dokoki tabbatar da zaben babban mai hamayya da shi na jam'iyyar Democrat Joe Biden.

Daga bisani ya shaida wa manema labarai cewa tuhumar da ake yi masa "na da alaka da siyasa".

Wannan ne karo na uku da tsohon shugaban kasar ta Amurka ya gurfana a gaban kotu bisa zagin aikata manyan laifuka a cikin wata hudu.

TRT Afrika da abokan hulda