Miliyoyin Amurkawa ne suka nufi rumfunar zaɓe a faɗin ƙasar ranar Talata domin kaɗa ƙuri'a a zaɓukan shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokokin ƙasar.
Mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris da ɗan takarar jam’iyar Republican Donald Trump suna fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa inda yawancin ƙuri'un jin ra'ayin jama'a ke nuna tazarar kashi ɗaya zuwa uku cikin ɗari a tsakaninsu.
Ƙuri'un jin ra'ayin jama'a biyar sun nuna cewa 'yan takarar biyu sun yi kankankan.
Fafatawar za ta ƙara zafi idan aka yi la'akari da muhimman jihohi bakwai da ka iya faɗawa a hannun ko wanne daga cikin 'yan takarar biyu inda ƙuri'un jin ra'ayin jama'a a jihohi huɗu — Nevada da Wisconsin da Michigan da kuma Pennsylvania — suka nuna tazarar kashi ɗaya cikin ɗari ko kuma ƙasa da haka tsakanin 'yan takarar.
Trump yana da ɗan rinjaye a jihohin Arizona da Georgia da kuma North Carolina, duk da haka yana gaba ne da kasa da kashi uku cikin dari.
Trump ya sha alwashin jagorantar Amurka "zuwa wani sabon matsayi na ɗaukaka" yayin da Kamala Harris ta nemi Amurkawa su yi zaɓen "da ya fi zafi a tarihi" yayin da 'yan takarar biyu suka kammala tallata kansu a yaƙin neman zaɓen.
Jihohin da ba a san mai rinjaye ba na da muhimmanci saboda saɓanin yawancin ƙasashen duniya masu bin tafarkin dimokuraɗiyya, Amurka ba ta zaɓen shugabanta kai-tsaye. Maimakon hakan ana zaɓen mambobin kwamitin masu zaɓen daga jihohi inda wakilai 538 ke kaɗa ƙuri'unsu bisa sakamakon zaɓen da aka yi a jihohinsu.
Kujerun majlisar wakilai da na dattawa
Ko wanne daga cikin 'yan takaran na buƙatar ƙuri'un 'yan kwamitocin zaɓe 270 daga jihohi don samun nasara. Ana bai wa jihohi 'yan kwamiti ne bisa yawan jama'arsu, kuma yawancin jihohi na bai wa wanda ya yi nasara a zaɓen gama-gari dukkan ƙuri'unsu.
Sai dai kuma irin wannan tsarin kaɗa ƙuri'u ga wanda ya yi nasara a zaɓen gama-gari ba a bin sa a jihohin Nebraska da Maine, waɗanda ke ba da ƙuri'unsu bisa yawan ƙuri'un da 'yan takara suka samu a zaɓukan gama-gari.
A wani bangare na zaben kuma masu zabe za su zabi 'yan majalisun da za su kasance a majalisar dokokin kasar.
A majalisar dattawa, za a yi zaben cike kujeru 34. Ana zaben sanatoci ne na wa'adin shekara shida, kuma ana zaben kashi daya cikin ukunsu a ko wane shekaru biyu. Kimanin hudu daga cikin kujerun ne ake ganin babu tabbacin wanda zai lashe su ciki har da fafatawa a jihohin Michigan da Ohio da Pennsylvania da kuma Wisconsin wadanda a halin yanzu suke hannun 'yan jam'iyyar Democrats.
'Yan Republican suna da dan fifiko wajen samun rinjaye a majalisar wakilai, amma duk wanda ya yi nasara zai yi fama da rashin tabbas na rinjaye mai rauni. A majalisar dattawan mai kujeru 100 jam'iyyu suna bukatar kuri'u 60 maimakon 50 kafin su iya mayar da kuduri doka.
Za a yi zaben cike dukkan kujeru 435 na majalisar wakilai, kuma kamar a majalisar dattawa, yawancin hasashe sun nuna cewa majalisar za ta rabu gida biyu ne tsakanin jam'iyyun. Wasu 'yan gwamman kujeru ne za su tabbatar da wanda zai yi rinjaye tsakanin 'yan Republicans da 'yan Democrats.
A matakin jiha da kanan hukumomi, masu zabe za su yanke shawara kan shirye-shirye da batutuwa daban daban. Za a yi zabukan gwamna na jihohi 11 a fadin kasar.