Za a ɗauki kwanaki kafin samun cikakken sakamakon babban zaɓen Amurka na 2024. / Hoto: DPA / Photo: Reuters

Daga Mazhun Idris

Saɓanin zaɓukan baya, zaɓen shugaban ƙasar Amurka na 2024 ya haifar da matsananciyar fargaba, kamar yadda Nicole wata mata baƙar fata 'yan shekara 25 da ke jihar Wisconsin a yamma ta tsakiyar Amurka, take gani.

"Yanayin zaɓen bana ya yi zafi, a fili da kuma a soshiyal midiya," cewar Nicole, wadda babbar ɗaliba ce a Jam'iar Wisconsin Madison.

Nicole ta ƙara da cewa "za ta so a kammala zangon zaɓen na bana komai ya wuce."

'Lokaci mai haɗari'

Ta bayyana damuwarta game da haƙƙoƙinta a matsayinta na mace baƙar fata, kuma tana da irin wannan damuwa ga al'umma baƙar fata a faɗin ƙasar.

Wannan ya dace da tunanin wasu cikin al'ummar baƙar fata da ma sauran tsirarun ƙabilu na ƙasar.

Irin wannan rashin kyakkyawan fata da masu zaɓe baƙar fata ke da shi, ba sabo ko baƙon abu ba ne, yayin da manyan 'yan takara ke nuni da lokacin zaɓen a matsayin "lokaci mai haɗari" ga Amurka da al'ummarta.

Zaɓen Amurka na 5 ga Nuwamban 2024 shi ne zaben shugaban ƙasa karo na 60 a tarihi. Miliyoyin masu zaɓe za su zaɓi shugaban ƙasa da mataimaki, da wa'adin shekara huɗu, wanda zai fara daga Janairun 2025.

Zaɓen wuri

'Yan takarar manyan jam'iyyu biyu suna neman gaje kujerar shugaba Joe Biden, ɗan jam'iyyar Democratic, wanda ya fita daga takarar a watan Yuli.

Mataimakiyar Shugaban ƙasa Kamala Harris tana takara ƙarƙashin jam'iyyar Democrat, tare da Tim Walz, gwamnan jihar Minnesota.

Donald Trump, wanda ya mulki Amurka a baya amma ya faɗi zaɓen neman wa'adi na biyu a 2021, yana takara tare da James David Vance, sanata daga Ohio, don sake shiga White House.

Kwana guda kafin zaɓe, fiye da mutane miliyan 75 daga jimillar masu zaɓe kusan miliyan 244 sun kaɗa ƙuri'arsu ta hanyar zaɓen wuri.

'Matuƙar gogayya'

Mabambantan ƙuri'o'in jin-ra'ayin jama da aka gudanar sun nuna cewa takarar tsakanin Kamala Harris da Donlad Trump za ta kasance mai "matuƙar gogayya."

Amma duk da kanfe ɗin zaburar da baƙar fata su shiga harkar zaɓe, al'ummar suna tararrabin abin da ka iya faruwa bayan zaɓen.

Nicole tana tsoron cewa za ta sha fama da mutane da za "su samu ƙarfin gwiwar daina ɓoye nuna wariyar launin fata", bayan sakamakon zaɓen na 2024.

Sai dai duk da haka, tana da cikakken imani da sahihancin tsarin zaɓen Amurka.

'Ɗan takara mai taimakon kowa'

Nicole ta ce, "Ina fatan kowa zai yi rijistar zaɓe ya kaɗa ƙuri'a don tabbatar da nasarar ɗan takarar da suka yi amanna zai taimake su, kuma ya taimaki al'mmarsu da ƙasa baki-ɗaya".

Ƙididdiga ta nuna cewa yawan fita zaɓe tsakanin baƙar fata yana sama da na al'ummar Latino da 'yan Asiya. A 2024, an yi hasashen adadin baƙar fata masu zaɓe ya kai miliyan 34.4, wato ƙarin kashi 7% daga adadin 2020.

Wannan na ɗaya daga dalilan da ake kallon masu zaɓe baƙar fata suna da babbar rawar takawa wajen fayyace sakamakon zaɓen bana.

An saba ganin zaɓen shugaban ƙasa a Amurka yana zafi tsakanin 'yan takarar Democratic da na Republican, inda suke kokawar isar da saƙonni mabambanta, game da batutuwa kamar na tattalin arziƙi, kiwon lafiya, baƙin haure, sauyin dokokin shari'a da na haraji.

Tsamarin siyasar duniya

Wannan shekarar, tsamarin siyasar duniya dangane da yaƙin Ukraine da na Gabas ta Tsakiya ya ƙara wa zaɓen Amurka tasiri.

Gwamnatin Amurka ƙarƙashin shugaba Biden da Harris, tana bai wa Ukraine goyon baya mara iyaka, yayin da saɓanin haka aka gani a Gabar ta Tsakiya, inda suka yi watsi da ta'asar da Isra'ila ke yi wa Falasɗinawa.

A gida Amurka, al'ummar baƙar fata ba za su manta da tarihin gwagwarmayar da suka yi wajen sauya tsarin mulki don samun 'yancin yin zaɓe ba.

Al'ummar baƙar fata ba su ga da sauƙi ba, game da batun 'yancin yin zaɓe, tun lokacin kafa ƙasar Amurka.

Sauye-sauyen shari'a

A tsarin mulki, ba a fayyace cewa Amurkawa baƙar fata suna da 'yancin yin zaɓe ba ba sai a shekarar 1870.

Sannan sai da aka samu sauye-sauyen tsarin mulki da sabbin dokokin majalisa kafin bai wa baƙar fata maza da mata 'yancin zaɓe, wanda ya faru lokacin sauye-sauyen shari'a da zamantakewar al'umma da aka yi a shekarun 1960s.

A zaɓen na bana, Kamala Harris tana neman zama mace ta farko baƙar fata da za ta zama shugabar Amurka.

A ɗaya ɓangaren, nasarar Donald Trump za ta sa ya zama tsohon shugaban ƙasa na farko da ya sake lashe zaɓe bayan shan kaye, tun a ƙarni na 19.

TRT Afrika