Da zarar wakilar masu zaɓe a Amurka suka tabbatar da nasarar Donald Trump na ranar 5 ga Nuwamba, 2024, za a rantsar da shi a kan mulki ranar 20 ga Janairu, 2025. / Photo: AP 

Daga Sylvia Chebet

Donald Trump ya sake samun damar lashe zaben shugaban Amurka a karo na biyu bayan hasashen sakamakon zaben da aka yi a ranar 5 ga watan Nuwamba wanda ya bayyana a ranar Larabar cewa ya samu ƙuri'u maki 270 da shan-kayen mataimakiyar shugaban ƙasar Kamala Harris.

Ɗan takarar jam’iyyar Republican ɗin ya maye rashin nasarar da yi a shekarar 2020 a muhimman jihohin Georgia, da Pennsylvania.

"Wannan shi ne mafi girman tafiyar siyasa da aka taba samu," a cewar Trump a yayin jawabin murnar nasararsa a cibiyar Taron Palm Beach County da ke Florida.

"Mun shawo kan matsalolin da babu wanda ya yi tunanin zai yiwu," in ji shi, yana mai gode wa magoya bayansa.

Trump ya fadada taswirar zaben jam’iyyar Republican, inda ya yi takarar shugabancin da ba a taba ganin irinsa ba tun shekara ta 1892 lokacin da aka zabi shugaban Amurka Grover Cleveland zuwa wa’adi na biyu da ba a jere ba a kan mulki.

An zabi mataimakin shugaban kasa Kamala Harris a matsayin yar takarar jam'iyyar Democrat bayan Shugaba Joe Biden ya fita daga takarar a watan Yuli 2024. / Hoto: Wasu

"Duba me ya faru, wannan mahaukaciya ce?" Trump ya fada yayin da aka yi masa tafi.

Hasashen farko kan zaɓen da aka yi ya nuna cewa Trump na kan hanyarsa ta lashe kuri'un da aka kada, in da shanye duk wani suka gami da yunkurin kisan kai yayin yakin neman zaɓe.

''Wannan gagarumin tarihi ne ga al'ummar Amurka da zai ba mu damar sake haɓaka Amurka.

"Tabbas wannan zai zama gwarzon lokacin Amurka.'' in ji shi.

Babban buri

Rayuwar Donald Trump daga ɗan kasuwa zuwa shugaban ƙasa na daya daga cikin manyan burinsa.

Trump ya kai ga zuwa babban ofishin ba tare da ƙwarewar siyasa ba a shekarar 2016.

Ya doke abokan hamayya da dama don lashe zaben fidda gwani a jam'iyyar Republican a lokacin zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa.

Ya kuma yi nasara wajen kayar da tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton a zaben shugaban kasa a lokacin ta hanyar lashe mafi yawan kuri'un wakilan masu zaɓe.

Hakan ya faru ne duk da cewa Clinton, 'yar takarar jam'iyyar Democrat ta lashe kuri'un da aka kada a muhimman jihohi a zaben ƙasar.

A matsayinsa na shugaban ƙasa, Trump ya sanya hannu kan wata babbar doka ta sake fasalin haraji tare da sa ido kan rage ka'idojin Amurka.

Manufofin kasuwancinsa sun haɗa da sanya haraji kan kuɗin fito a aluminium, ƙarafa, da sauran kayayyaki na ƙasashen waje

A 2020, Trump ya sha kaye a takarar zaben da sake tsayawa da ɗan takarar jam'iyyar Democrat Joe Biden wanda ya janye daga a ƙarshe da takarar shugaban ƙasa na shekarar 2024.

Za a rantsar da sabon shugaban na Amurka a ranar 20 ga Janairu, 2025.

US President-elect Donald Trump married Melania in 2005. /Photo: AP

Rayuwar ƙuruciyarsa

An haifi Donald Trump a New York a ranar 14 ga watan Yuni, 1946, ya kasance ɗa na huɗu ga mahaifinsa Fred Trump, wanda shahararren attajiri ne a fannin gine-gine da kuma mahaifiyarsa Mary Anne Trump, 'yar Scotland-Ba'amurkiya mai ba da taimakon jinƙai.

Ya halarci makarantar soji ta New York daga baya ya kammala karatun digirinsa a fannin kasuwanci daga Jami'ar Pennsylvania.

Bayan kammala karatunsa na jami'a, ya karbi jagorancin kamfanin mahaifinsa, inda ya sanya mata suna da Trump Organisation.

Daga baya ya fadada kasuwancin nasa zuwa wasu ayyuka da yawa, ciki har da buɗe otal-otal, da wuraren shakatawa, da gine-gine zama da na kasuwanci, da gidajen caca, da wasannin golf da dai sauransu.

A 2004, ya dauki nauyin shirin talabijin na "The Apprentice."

Ya auri Melania Knauss ;yar asalin Slovenia ce kuma mai tallan kayan ƙawa a 2005 kuma suna da ɗa ɗaya mai suna Barron.

Kazalika Trump na da 'ya'ya hudu daga auren biyu da da ya yi a baya. Yaran su ne Donald Jr. da Ivanka, da Eric, da kuma Tiffany Trump.

TRT Afrika