Daga Mazhun Idris
A 2018, shafin wallafa bidiyo a intanet na YouTube ya fito da wani tsari mai nufin ƙarfafa bayyana gaskiya ga masu amfani da shafin.
Wannan fasalin ya ba wa shafin damar nuna idan bidiyon da aka wallafa a shafin an "yi shi ne da kuɗin al'umma ko na gwamnati".
Idan wani ya ɗora bidiyon da aka yi da irin wannan kuɗaɗen, ya kamata a ga wata sanarwa ta fito a ƙasan bayanan taken bidiyon. Sanarwar za ta ƙunshi mahaɗin da ke kaiwa ga shafin Wikipedia na kafar sadarwar da ta wallafa.
Alal misali, a ƙarƙashin bidiyon da kafa kamar BBC ta wallafa, wata sanarwa za ta bayyana, mai cewa, "BBC kafar Burtaniya ce mallakin gwamnati."
Sanarwar takan kuma fito a duk wata wallafa da wasu kafafen sadarwa na gwamnati suka saka.
Sauran shafukan sada-zumunta kamar Facebook, sun fito da irin wannan tsarin na sanarwa tun a 2019, wadda nufinta shi ne bambance kafofin da "gwamnatoci ke iko da su ɗungurungun ko kuma wani ɓangare".
Wani hanzari shi ne, idan ka buɗe bidiyon shafin cibiyar "BBC Media Action" na YouTube, wadda wani shiri ne na ayyukan tallafi da cigaba, wanda BBC ta assasa a 1999, ba za ka ga irin sanarwar da ke cewa da kuɗin jama'a aka yi bidiyon ba.
Matsalar karɓar kuɗi
Ranar 2 ga Fabrairu, babban abokin shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya mallakin shafin X wato Elon Musk, ya wallafa a shafinsa cewa cibiyar USAID ta yi ta amfani da dalolin al'umma wajen biyan "kafofin yaɗa labarai don su wallafa farfaganda".
Elon Musk ya sake jaddada zarge-zargen nasa bayan kwanaki huɗu, inda ya ambaci suna yana cewa. "Me ya sa ake amfani da kuɗin al'ummar Amurka wajen ɗaukar nauyin BBC?".
Shugaba Trump ya bi sahun Elon Musk, inda ya zargi USAID da bai wa gidajen jaridu kuɗi don fifita jam'iyyar Democratic Party.
Waɗannan bayanai na abin kunya sun fito da munafurcin da kafafen sadarwa na Yammacin duniya ke yi wajen saka-ido kan ayyukan jarida a duniya, musamman a Afirka
Kakakin BBC Media Action ya yi bayani ga Reuters cewa duk da cibiyar tana karɓar kuɗi daga USAID da sauran masu ba da kuɗi, shirin wani ɓangare ne kawai na jin-ƙai na BBC, kuma yana "cin gashin-kansa kuma ba shi da alaƙar aikin jarida da kafar labarai ta BBC".
Wata sanarwar yaɗa labarai tasu ta yi iƙirarin cewa "BBC Media Action shiri ne da ke tallafa wa gidajen jaridu na ƙasashen duniya, don isar da amintattun bayanai ga al'ummar da ke buƙata".
Rasa kima
Yayin da badaƙalar USAID da BBC ke fitowa fili, akwai ƙarin damuwa kan yadda ake sauya fahimtar mutane da amfani da kuɗaɗe don yaɗa farfaganda.
Ƙasashen Afirka sun fi samun cutuwa daga irin wannan tsari na nuna fifiko.
Wani marubuci kuma mai shirya fina-finai ɗan Ghana, Dwomoh-Doyen Benjamin ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "To wa yake fayyace mene ne 'amintattun bayanai' — masu ba da ƙudin, ko kafofin yaɗa labaran?"
Benjamin, wanda shugaban African Chamber of Content Producers ne, ya ce, "Waɗannan bayanai na abin kunya sun fito da munafurcin da kafafen sadarwa na Yammacin duniya ke yi wajen saka-ido kan ayyukan jarida a duniya, musamman a Afirka.
Babbar tambayar ita ce: Shin gwamnatin Amurka ta ɗauki nauyin babbar kafar watsa labarai ta Burtaniya, ko a'a?
Idan BBC ta iya gujewa alhakin "taimakawa kisan-kiyashin Isra'ila a Gaza", shin shugabannin BBC sun amsa cewa sun rasa aminci, saboda cakwakiyar da suka shiga ta farfagandar manufofin diflomasiyya?
Girman ɓarna
Bisa la'akari da kalaman gwamnatin Amurka ta yau kan BBC, an dakatar da duk wasu kuɗaɗe da USAID ke bai wa shirye-shiryen BBC, wanda a baya ya kai kusan kashi 8% na jimillar kuɗin da suke samu.
Abin da hakan ya gadar shi ne, ana kallon ƙurilla a bainar jama'a ga wata babbar kafar watsa labarai da take alfahari da kanta a matsayin "mara nuna son-kai kuma mai zaman-kanta".
"A yayin wannan abin kunya mai rikitarwa, BBC ta rasa 'yancin gashin-kanta da 'yancin faɗar ra'ayinta," cewar Abubakar Muhammad, wani ɗalibin babban digiri a Jami'ar Wisconsin-Madison, wanda ya zanta da TRT Afrika.
Gwada cire sunan BBC, sannan ka saka sunan wata kafar yaɗa labarai ta jama'a a wata ƙasa mai tasowa, wadda aka zarga da karɓar kuɗi daga gwamnatin wata babbar ƙasa.
Iƙirarin da za a yi shi ne cewa an samu wadatattun hujjojin da ke nuna cewa ayyukan watsa labarai na kafar ya zama mai nuna son-kai, kuma mara aminci.
Sauya tunani a ɓoye
Abin lura shi ne, farfaganda ba salo guda ne da ita wanda yake taƙaita ga ɗakunan watsa labaraia kawai ba.
Ana iya isar da farfaganda a duka ayyukan gidajen jarida — kama daga sharhin labarai, da tsarin yin labarai, da tsara shirye-shirye.
Ana iya murɗa tunanin al'umma ta hanyar zaɓar bayanan da ake fitowa da su, da zaɓar mahangar da ake jaddadawa, da kawar da wasu bayanai, da shirya zubin batutuwa, da janyo tsana, da assasa soyayya, da rufe baki ko toshe wasu kalamai.
A tsarin zamani da ake amfani da jarida a matsayin makami, yaɗa labaran ƙarya ba ya tsayawa kan yaɗa ƙarya kawai don ɓata suna.
Yaɗa bayanan ƙarya wani makami ne mai ƙarfi, haka ma salon ba da fifiko kan wani abu, ko yawan maimaita wasu zaɓaɓɓun bayanai ko mahanga.
Masana cigaban duniya suna nuni da cewa, ana yawan amfani da shirye-shirye masu zummar jin-ƙai, don kau da ido daga shirye-shiryen leƙen-asiri, wanda ake yi don yaudarar masu amfana, domin cim ma wasu manufofi.
Misali, ƙungiyoyi masu ba da tallafin kuɗi ba lallai su nemi yin iko na kai-tsaye da shirin da suke ɗaukar nauyi ba, matuƙar dai an shigar da ajandarsu cikin ƙa'idojin yarjejeniyar karɓar kuɗinsu.
Ko ma mene ne, irin wannan ajandojin ba sa daidai da tsarin tace labarai.
Tabbas, babu wata matsala idan saboda fito da gaskiya an binciki manyan gidajen jarida kamar BBC, don fayyace matsayar da suke alfahari da ita cewa su 'tushe ne mai 'yanci na samun labarai ba tare da nuna son-kai ba'.