Sabon matakin da kamfanin Twitter ya dauka na takaita adadin sakonnin da masu amfani da shafin za su iya gani a kullum, ya sa mutane musamman a kasashe irin Nijeriya sun fara tunanin ina za su koma baje-kolinsu idan manyan shafukan soshiyal midiya suka ci gaba da kawo irin wannan tsarin.
Twitter ya ce ya dauki wannan mataki ne da zummar rage "yin almubazzaranci" da sakonni da kuma yin abin da bai dace ba, a cewar shugaban kamfanin Elon Musk.
Kamfafen sada zumunta sun zama wani muhimmin sashe na rayuwar miliyoyin jama’a saboda kusan duk wani lamari na rayuwa ana yi da su.
Kafafen Facebook da Twitter da Instagram suna daga cikin wadanda suka fi yin fice inda mutane ke sada zumunta da kasuwanci da karatu da abubuwa da dama na rayuwa.
A duk lokacin da wadannan kafafe suka samu tsaiko ko kuma sauyi ko na lokaci kadan ne, hankalin jama’a kan tashi sakamakon sabo da kuma yadda aka mayar da su wani sashe na rayuwa.
Matakin na Twitter sun ta jawo ce-ce-ku-ce da kuma barazana ga masu amfani da shafin a ‘yan kwanakin nan.
Tun bayan da kamfanin ya koma hannun shahararren mai kudin nan Elon Musk, masu amfani da shafin suka soma neman mafita sakamakon matakin kamfanin na farko na korar ma’aikata da dama.
Bayan haka kamfanin ya ci gaba da daukar matakai iri daban-daban wadanda suke shafar masu amfani da shi kai tsaye.
Matakin shugaban kamfanin na Tesla na mayar da shudin makin tantance masu amfani da shafin Twitter na sayarwa ya kara sa jama’a kara baya-baya da shafin, inda da dama suka rinka korafi kan cewa matakin zai rage wa shafin armashi.
Sai kuma kwatssam ga matakin nan na takaita adadin sakon da masu amfani da shafin za su iya gani a kullum.
Neman mafita
Twitter ya zama wani dandali tamkar jini da tsokar mafi yawan 'yan Nijeriya, kuma waje ne da aka san shi da raha da gatse da iya kwarmata duk wani maudu'i da ke tashe a kowane lokaci.
Waje ne da wasu da dama ke ganin da a ce za a wayi gari an rufe shi baki daya da hakan ka iya shafar walwalar wasu da dama.
A lokacin da aka yi rikicin Endsars a Nijeriya, gwamnatin kasar ta saka takunkumi kan shafin Twitter, lamarin da ya jawo ‘yan kasar masu amfani da shafin suka soma neman mafita.
Duk da gwamnatin kasar ta haramta amfani da shafin, wasu kan bi ta bayan gida ta hanyar amfani da VPN domin shiga shafin.
Sai dai wasu ‘yan kasar irin su Adamu Garba, wani fitacce a duniyar Twitter a Nijeriya, sun fito da shafin sada zumunta na musamman don 'yan kasar su koma can su ci gaba da zumuncinsu da suka saba.
Amma duk da haka, shafin na Adamu Garba mai suna Crowwe ya rinka samun kalubalen da har suka sa ya daina aiki.
Akwai masu irin wadannan shafukan sada zumunta wadanda da sun fara sai ya ki dorewa ko kuma ya rinka fuskantar matsaloli.
Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump shi ma yana da kamfaninsa na Truth Social wanda shafi ne na sada zumunta na kashin kansa da ya bude, sakamakon rashin jituwa da ya rinka samu da kamfanin Twitter tun lokacin da kamfanin ke hannun Jack Dorsey.
Shi ma a ‘yan kwanakin nan shafin nasa ya rinka samun matsala.
Kalubalen da sabbin shafukan sada zumunta ke fuskanta
Wanda ya kirkiro da shafin sada zumunta na Crowwe Adamu Garba ya shaida wa TRT Afrika cewa akwai son rai na masu kula da mazaunin shafin da ke kan yanar gizo.
“Ita kanta manhajar tana zama a abin da ake kira cloud, wata fasaha ce wadda take zama a kan yanar gizo, ita wannan fasahar, akwai wadanda suke kula da matattarar ajiye bayananta,” in ji Adamu Garba.
Ya ce wadannan kamfanonin su ne ke ba su damar dora shafukansu a yanar gizo.
“Idan tsarin mutum ya sha bamban da nasu shi ne wani lokaci sai su kawo matsaloli da zai sa nakan su rushe saboda ka da a yi amfani da shi.
"Misali su sun amince mutane su rinka barin wadanda suke kiran kansu da ‘yan luwadi ko madigo su tallata kansu a wurin, ku kuma ba ku yadda da wannan ba.
“Idan aka samu bambancin ra’ayi sai su iya takura wa naku sai ya samu matsala,” in ji Adamu Garba.