Illustration shows blue verification badge, Facebook and Instagram logos / Photo: Reuters

An shafe kusan mako guda ana muhawara a duniyar Facebook ta arewacin Nijeriya kan batun biyan kudi don tantancewa da samun alamr sahihancin shafin Facebook na mutane daga kamfanin Meta.

Shafin Facebook ya yi ta tura wa mutane saƙo na cewa sun cancanci samun alamar tantancewar da ake kira “Blue Tick”, wato “Shudin Maki”, amma fa sai sun dinga biyan kudi har Naira 4,500 duk wata.

A baya, Facebook kan bai wa masu amfani da shi “Blue Tick” ne ta yin duba da yawan mabiyansu da irin abubuwan da suke wallafawa da kuma yawan tsokacin da ake yi musu, amma daga baya suka bi sahun shafuka irin su Twitter da yanzu ya koma X, suka mayar da lamarin “iya kudinka, iya shagalinka.”

Batun biyan kudin ya jawo ce-ce-ku-ce da muhawara sosai a duniyar Facebook ta arewacin Nijeriya, inda wasu ke cewa ba za su iya biyan kudi don kawai su samu “Blue Tick” ba, wasu kuma ke ganin babu faduwa a yin hakan.

Mene ne amfanin “Blue Tick”?

Kamfanin Meta ya samar da tsarin tantance mutum ta hanyar sanya Shudin Maki a gefen sunansa a shafin ne don nuna cewa shafinka sahihi ne, tare da bambance shi daga shafukan ƙarya da ake buɗewa da sunanka.

Hakan zai sa mabiyanka su yi saurin gane shafinka na ainihi tare da gudun faɗa wa tarkon masu sojan gona da kuma masu amfani da sunan fitattun masu amfani da shafin wajen damfarar wasu mutanen.

Haka kuma, wasu da dama na ganin samun alamar tantancewar wata daraja ce da ke ƙara musu ƙima a duniyar ta Facebook.

Me mutane ke cewa a kan batun?

An kusa mako guda ana tattauna wannan batun a Facebook, har ya kasance kalmar “Blue Tick” ta zama daga cikin mafiya tashe a kafar.

Wasu daga cikin wadanda suka samu damar sayen “Blue Tick” sun yi ta yin shagube ga wadanda suke korafin cewa ba za su iya saye ba, yayin da su kuma wadancan suke ganin “nuna isa da alfahari ne” kawai ya sa mutane suke saya bisa ƙarfin hali don kar a ga gazawarsu.

Da dama kuma tambaya suke wane amfani ko tasiri sayen "Blue Tick" zai yi a rayuwar mutane da har wasu ke ganin ya zama dole su saya.

Sannan wasu na cewa sayen nasa na da muhimmanci musamman ga mutanen da ke yin kasuwanci sosai a Facebook kuma suna so kasuwancin nasu ya kara shahara.

Ga dai wasu daga cikin ra’ayoyin da aka bayyana a Facebook ɗin:

Bluetick
Bluetick
Bluetick
Bluetick
Bluetick
Bluetick
TRT Afrika