Ɗan takarar Jam'iyyar Republican Donald Trump a ranar Laraba ya sha alwashin "warkar da" kasar bayan da ya yi ikirarin samun nasara a kan abokiyar hamayyarsa na Jam'iyyar Democrat Kamala Harris a daya daga cikin zabukan da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Amurka.
“Ƙasarmu na buƙatar taimako, kuma tana buƙatar taimako sosai-sosai. Za mu gyara al’amura a kan iyakarmu, kuma za mu gyara dukkan abin da ya lalace a ƙsarmu,” kamar yadda Trump ya shaida wa taron magoya bayansa da ke cikin farin ciki a hedƙwatar yaƙin neman zaɓensa a Florida.
Ya yi jawabin ne jim kadan bayan da tashar talabijin ta Fox News mai ra’ayin ‘yan mazan jiya ta ce shi ya ci zaɓen, yayin da sakamakon daga fadin kasar ke ta bayyana suna nuna shi ne a kan gaba da Harris.
“A yanzu a bayyane yake cewa mun cim ma wani gagarumin abu na siyasa... kalli abin da ya faru, hakan hauka ne?” kamar yadda Trump ya bayyana.
A hedkwatar kamfe dinsa da ke West Palm Beach a Florida, Trump ya yi wa Amurkawa alkawari cewa, "Kowace rana, zan tare muku fada," kuma ya ce zai kawowa Amurka gagarumin ci gaba da shigar da ita “gwarzon lokaci.”
Trump ya halarci wajen ne ƙarƙashin rakiyar iyalansa da matarsa Melania Trumo ta jagoranta, da mataimakinsa na shugaban kasa JD Vance da kuma aminansa.
Trump ya kuma yabi wasu shahararrun mutane a kan dandalin. Trump ya kuma yi wa Elon Musk kirari, hamshakin attajiri mamallakin shafin X, wanda ya zama daya daga cikin manyan magoya bayansa.
“Muna da sabon taurari. An haifi tauraro: Elon,” in ji Trump.
'Dakatar da yaƙe-yaƙe'
Trump, wanda zai kasance tsohon shugaban kasa na farko da zai koma kan karagar mulki tun lokacin da Grover Cleveland a shekarar 1892, ya ce yana "aiki ne don dakatar da yake-yake", ba wai ya fara wasu ba.
"Mun fatattaki ISIS (Daesh) a cikin ɗan lokaci, amma ba mu yi yaƙe-yaƙe ba. Sun ce: 'zai fara yaƙi.' Ba zan fara (ko ɗaya ba), (Ina) aiki don dakatar da yake-yake amma wannan kuma babbar nasara ce ga dimokuradiyya da kuma 'yanci, "in ji shi.
Da yake jaddada cewa zama shugaban Amurka shi ne "aiki mafi mahimmanci" a duniya, Trump ya yi ikirarin cewa yana da "abin kirki sosai" a wa'adi na farko.
"Ba wani abu da zai hana ni cika alkawarina gare ku jama'a. Za mu sake mayar da Amurka mai aminci mai karfi, da wadata, da kuma 'yanci.
Trump ya kasance mutum na farko da aka taba zaɓa bayan samunsa da laifin aikata wani laifi a matsayin shugaban kasa kuma a shekarusa 78 ya kasance mutum mafi tsufa da aka zaba a ofishin.
Mataimakinsa a takarar, JD Vance mai shekaru 40 ya fito ne daga jihar Ohio, kana zai zama memba mafi girma mai karancin shekaru a gwamnatin Amurka.
Trump ya yaba da nasarar jam'iyyar GOP na Republican
Trump ya kuma tabbatar tare da amincewa da nasarar jam'iyyar Republican a zaɓen da aka gudanar a cikin jawabin nasa.
"Yawancin nasarorin da aka samu a majalisar dattijai abu ne mai matukar ban mamaki," in ji Trump.
Ya zuwa yanzu dai 'yan jam'iyyar Republican sun samu kujeru 51, wanda ya basu rinjaye. Sai dai kawo yanzu ba a bayyana sakamakon jihar Montana, da Wisconsin, da Michigan, da Pennsylvania da kuma Nevada ba, kuma akwai yiwuwa 'yan Republican na iya samun ƙarin kujeru.
Trump ya kuma ce yana sa ran 'yan jam'iyyar Republican za su rike majalisar, yana mai yaba wa kakakin majalisar Mike Johnson.