Mataimakiyar shugaban Amurka kuma 'yar takarar Jam'iyyar Democrat Kamala Harris ta yi alkawarin mika mulki cikin lumana ga Donald Trump a jawabinta mai sassauci.
"Dole ne mu amince da sakamakon wannan zabe. A yau, na yi magana da zababben shugaban kasa Trump tare da taya shi murnar nasarar da ya samu," in ji Harris a jawabin da ta yi a Jami'ar Howard anWashington.
"Na kuma gaya masa cewa za mu taimaka masa da tawagarsa wajen miƙa mulki, kuma za mu gudanar da komai cikin lumana yayin miƙa mulki."
2238 GMT — Obama ya taya Trump murnar nasarar da ya yi kan Harris
Tsohon shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya taya Donald Trump murnar lashe zaben da ya yi, inda ya bayyana muhimmancin miƙa mulki cikin lumana.
"Wannan ba shakka ba shi ne sakamakon da muka yi fata ba," in ji Obama a cikin wata sanarwa. "Amma rayuwa a cikin dimokuradiyya ita ce fahimtar cewa ra'ayinmu ba ko yaushe zai yi nasara ba, da kuma kasancewa a shirye mu amince da miƙa mulki cikin lumana."
1517 GMT — Harris za ta yi wa Trump waya ta amsa shan kaye a zaɓe — rahoto
Ana sa ran mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris za ta kira Donald Trump a waya a ranar Laraba domin amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasar, kamar yadda tashar NBC News ta ruwaito, inda ta ambato wasu mataimakan Harris guda biyu da suka fadi hakan.
Shugaba Joe Biden kuma yana shirin kiran Trump kuma zai yi magana a bainar jama'a game da sakamakon zaben, in ji NBC News, yana ambato wani jami'in Fadar White House.
Ana kuma sa ran za ta gabatar da jawabi a karfe 1100 na dare agogon GMT, kamar yadda majiyoyi biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
1849 GMT - Harris ta kira Trump, ta amince da shan kaye a zaben shugaban kasa na Amurka
Mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris ta kira Donald Trump domin taya shi murnar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar na shekarar 2024, kamar yadda daya daga cikin manyan mataimakanta ta ce, biyo bayan fafatawar da suka yi da juna.
'Yar Jam'iyyar Democrat Harris ta tattauna da Trump kan muhimmancin miƙa mulki cikin lumana da kuma zama shugaban kasa ga dukkan Amurkawa, in ji mataimakiyar da take magana a baya.
An sake zaɓar Trump a matsayin Shugaban Ƙasar Amurka na 47
A ranar Laraba ne aka zabi Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka na 47, lamarin da ya zama babban tagomashi ga tsohon shugaban kasar da ya ƙi amincewa da shan kaye shekaru hudu da suka gabata, inda aka same shi da aikata manyan laifuka, kuma ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kisa har sau biyu.
Kamfanin dillancin labaran AP ya bayar da rahoton cewa, bayan samun nasara a Wisconsin, Trump ya samu ƙuri'u 270 na zabe da ake bukata domin ya zama shugaban kasa.
Trump shi ne tsohon shugaban kasa na farko da ya sake komawa kan karagar mulki tun lokacin da Grover Cleveland ya sake samun damar komawa Fadar White House a zaben 1892.
Tun kafin a sanar da nasarar a hukumance, dan takarar Republican ya ayyana samun nasara a kan 'yar takarar Democrat Kamala Harris.
"Mun kafa tarihi saboda dalili a daren yau, kuma dalilin zai kasance kawai mun shawo kan cikas da babu wanda ya yi tunanin za su yiwu," Trump ya fada wa magoya bayansa cikin farin ciki a Florida. "Nasarar siyasa ce da kasarmu ba ta taba gani ba."
Da yake gode wa jama'ar Amurka saboda "girmamawar ban mamaki na zabensa a matsayin shugaban kasa na 47", Trump ya ce: "Wannan babbar nasara ce ga jama'ar Amurka".
Harris, wacce har yanzu ba ta bayyana amincewa da shan kaye ba, ba ta yi magana da magoya bayanta ba, wadanda suka taru a Jami’ar Howard da ta yi karatu. Shugaban yakin neman zabenta, Cedric Richmond, ya yi jawabi da tsakar daren Talata, yana mai cewa Harris za ta yi magana a bainar jama'a ranar Laraba.
Trump ya yi iƙirarin nasarar komawa karagar mulki
Dan takarar jam’iyyar Republican, Donald Trump, ya bayyana cewa shi da magoya bayansa sun kafa tarihi ranar Laraba a zaɓen shiga Fadar White House, inda ya yi iƙirarin doke abokiyar hamayyarsa ta Jam’iyyar Democrat Kamala Harris a zaɓen shugaban kasar Amurka.
Nasarar za ta kasance komawa karagar mulki mai cike da ban mamaki shekara hudu bayan ya bar Fadar White House.
"Akwai dalilin da ya sa muka kafa tarihi a wannan daren, kuma dalilin shi ne mun ƙetare matsalolin da babu wanda ya yi tunanin cewa za a iya tsallake su," in ji Trump ga magoya bayansa da ke cike da farin ciki a Florida. "Nasara ce ta siyasa da kasarmu ba ta taɓa gani ba."
Yayin da yake gode wa mutanen Amurka domin “muhimmin karamcin zaɓena a matsayin shugaban Amurka na 47 ”, Trump ya ce: “Wannan wata babbar nasara ce ga mutanen Amurka”.
Kafar Fox News ta ayyana Trump a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban Amurka ranar Laraba — kafa daya tilo da ta yi wannan iƙirarin.
Sauran kafafan watsa labarai ba su ayyana Trump a matsayin wanda ya yi nasara ba tukunna, amma alamu sun nuna cewa yana daf da yin nasara bayan ya yi nasara a jihohin raba-gardama na Pennsylvania da North Carolina da kuma Georgia yayin da yake kan gaba wasu jihohi hudun kuma, in ji Edison Research.
Harris ba ta gabatar da jawabi ga magoya bayanta da suka taru a jam’iar Howard inda ta yi karatu ba. Daya daga cikin shugabannin yaƙin neman zaɓenta, Cedric Richmond, ya dan gabatar da jawabi bayan karfe 12 na dare inda ya ce Harris za ta yi bayani ranar Laraba.
Yadda hankalin duniya ya koma kan zaɓen Amurka
Jirage marasa matuƙa na ta shawagi a sararin samaniya sannan gwanayen harbi daga ɓoye suna ta sa ido a yayin da miliyoyin Amurkawa suka kaɗa ƙuri'unsu a ranar Talata a zaɓen Amurka da ya fi kowanne jawo rarrabuwar kawuna a tarihi.
Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris da ɗan takarar Jam'iyyar Republican Donald Trump suna fafatawa a zaɓen wanda ke matuƙar jan hankali.
Idan Trump ya yi nasara zai zamo shugaban ƙasa na farko da aka taɓa tuhuma da aikata manyan laifuka.
Trump zai kuma zamo shugaban ƙasa na biyu a tarihi da zai yi wa'adai biyu ba a jere ba a matsayin shugaban ƙasa, bayan Grover Cleveland a ƙarshen ƙarni na 19.
Ita kuwa Haris tana fatan zama mace ta farko, kuma mace baƙar fata ta farko, sannan 'yar asalin yankin Asiya ta farko da za ta shiga Fadar White House.
Jami'ai sun samar da matakan tsaro a rumfunan zabe a faɗin ƙasar a ƙoƙarinsu na tabbatar da cewa komai ya gudana cikin aminci.
Don ƙara ƙarfafa tsaro, an girke 'yan sanda da dama a kan tituna a faɗin ƙasar.
Trump yana kan gaba a zaɓen shugaban Amurka, Harris na biye da shi
'Yar takarar Democrat Kamala Harris da takwaranta na Republican Donald Trump suna fafatawa domin shiga Fadar White House, inda aka rufe rumfunan zaɓe ranar Talata sannan ake jiran tsammani na sakamakonsa.
Ƙwarya-ƙwaryar sakamakon zaɓen da kamfanin dillancin labaran The Associated Press ya tattara ya nuna cewa Trump yana kan gaba a jihohi 19, yayin da Harris ke kan gaba a jihohi goma.
Hakan na nufin Harris na da ƙuri'u 99 na wakilan da ke zaɓen shugaban ƙasa yayin da Trump ya samu ƙuri'u.
Ana buƙatar ƙuri'u 270 kafin mutum ya zama shugaban ƙasa.
Trump yana kan gaba a jihohi 9, Harris tana da jihohi 5 — ƙwarya-ƙwaryar sakamako
Ƙwarya-ƙwaryar sakamakon zaɓen da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya tattara ya nuna cewa ɗan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Republican Donald J Trump yana kan gaba a jihohi tara, yayin da 'yar takara ta Democrat Kamala Harris take kan gaba a jihohi biyar.
Associated Press ya yi hasashen ne gabanin a kammala jefa ƙuri'a.
Miliyoyin Amurkawa ne suke kada ƙuri'a a fafatawar da ake yi tsakanin Trump da Harris.
Kazalika ana zaɓen 'yan majalisar dokokin tarayya.
2115 GMT — Ana ci gaba da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa
Wakiliyar TRT World Zahra Yarali ta rawaito daga garin Fairview na jihar Virginia yadda masu fafutukar goyon bayan Falasdinawa suka fito a rumfunan zabe.
Sun isa rumfunan zabe biyar na yankin DMV (DC, Maryland, Virginia) inda suka rika kira ga masu kada kuri'a su tuna da kisan kare-dangin da Isra'ila take yi wa al'ummar Gaza kafin su jefa kuri'unsu.
Wata Ba'amurkiya 'yar asalin Falasdinu Hazami Barmada da sauran jama'a sun dauki kwalaye da ke alamta cewa ya kamata mutane su yi zabe na "dimokuradiyya.
1840 GMT — An kama mutumin da ya yi barazana a rumfar zaɓe a New York
An kama wani mutum bayan ya yi mummunar barazana a wata rumfar zabe da ke garin Fowler a birnin New York.
“Bincike ya tabbatar da cewa wani namiji wanda aka taɓa tuhuma da babban laifi ya yi yunkurin kada kuri’a, kuma matsayinsa ya nuna cewa ba shi da rajista tun bayan da aka sako shi daga gidan yari,” in ji sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, inda ta kara da cewa mutumin ya fusata kuma ya fara yin "kalamai masu ban tsoro cewa zai ƙona wurin kuma zai dawo da bindiga."
‘’Yan sanda sun kaddamar da bincike don neman mutumin, wanda ya gudu daga wurin, amma jim kadan aka kama shi.” Sanarwar ta ce, ana ci gaba da gudanar da bincike.
1702 GMT — Donald Trump ya kada kuri'arsa a Florida
Donald Trump ya kada kuri'arsa a Palm Beach, Florida kuma ya ce yakin neman zabensa na baya-bayan nan shi ne mafi kyau.
Da yake magana da manema labarai, Trump ya ce yana da "kwarin gwiwa" zai " lashe zaben."
"Na gudanar da gagarumin yakin neman zabe, ina ganin watakila shi ne ya fi kyau a cikin ukun, mun yi aiki mai kyau a na farko, mun yi a na biyu amma wani abu ya faru, zan ce wannan shi ne mafi kyawun yakin neman zaben da muka gudanar," in ji shi, yana tsaye kusa da matarsa, Melania Trump.
Ya ce zai amince da shan kaye "idan zabe ne na gaskiya".
1329 GMT — Ana ta ɗaukar matakai a Washington kan yiwuwar ɓarkewar rikici a zaɓen Amurka
Ana ta rufe harkokin kasuwanci a yankunan da ke kusa da Fadar White House stare da ɗaukar matakan tsaro yayin da ake taka tsantsan cikin fargabar ɓrkewar rikici a ranar zaben - da kuma kwanaki masu zuwa.
Magajin Garin DC Muriel Bowser ya ce hukumar 'yan sanda tana kuma ƙara ƙaimi a gundumomin kasuwanci da ke dukkan yankuna takwas na birnin.
Shugabar 'yan sandan birnin Pamela Smith a wani taron manema labarai ta kuma tabbatar wa mazauna birnin cewa sashenta ya shirya don tunkarar duk wani abu da ranar zabe za ta iya kawowa.
Ta ce, "Tawagarmu ta kasance da cikakkiyar himma da kuma taka tsantsan," in ji ta. "Mu ne mafi ƙwarewa a kasar nan kan abin da muke yi, kuma za mu ci gaba da aiki ba dare ba rana don kiyaye Washington DC, da kuma kiyaye mazaunanmu."