Daga Kristian Alexander
Alamu sun nuna zaɓen shugaban ƙasar Amurka na 2024 da aka yi wannan makon zai zamo wanda ya fi kowanne takun-saƙa a baya-bayan nan, wanda ya janyo gwagwarmaya tsakanin 'yan takarar da suka yi gogayya tsakaninsu.
Tsohon shugaba Donald Trump da mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris suna wakiltar mabambancin tunani game da ƙasar.
Trump yana da farin jini saboda kausasa magana kan kishin ƙasa, inda ya sha suka daga 'yan hamayya.
Ita kuwa Harris tana da salon neman 'yanci, sai dai rashin tabbasa game da fahimtarta kan lamuran duniya ya janyo mata suka.
Salonsu da aƙidarsu mai cike da bambanci sun ƙarfafa girman rarrabuwar siyasarsu, wanda ya haifar da martani zazzafa daga ɓangarorin siyasar ƙasar.
Ƙasar ta samu rarrabuwar kai matuƙa kan batun muhalli wanda ya janyo damuwa kan zaben 2024 zai iya hasala wutar rikicin siyasa, inda ƙungiyoyin tsattsauran ra'ayi da masu ra'ayin siyasa suke ribatar wannan rabuwar-kai.
Duka masu ra'ayin mazan jiya da na 'yan zamani sun nuna ƙaunar amfani da rikici don cim ma burukansu.
Suna amfani da rashin yarda da ake wa cibiyoyin gwamnati, da gidajen jarida, da jami'an tsaro.
Kafofin soshiyal midiya da wasu gidajen labarai sun zuzuta wannan yanayi, wanda ke harzuk labaran bogi da zargin munamuna wadda ke ta'azzara zargi da tsaurin ra'ayi.
Tunanin baya
Ana tuno ɓurɓushin abin da ya faru a zaɓen baya a wannan shekara. Ranar 6 ga Janairun, 2020, masoyan Trump da suke tunanin an yi maguɗi a zaɓen sun far ma majalisar Dokokin Amurka yayin da ake zaɓen tabbatar da nasara shugaba Joe Biden.
An lalata cikin ginin majalisar, kuma an jikkata mutane sannan wasu sun rasa rayukansu.
Boren yana tunatar da haɗarin rarrabuwar aƙida da ke iya haifar da rikici. Tun wannan abin da ya faru, an samu ƙaruwan hare-haren masu alaƙa da siyasa kan jami'ai, 'yan jarida, da gamagarin mutane.
Zanga-zanga kan batun adalcin zamantakewa wanda bangarorin masu son kawo canji ya koma tashin hankali da ya yi ta'adi a 2020.
Birane kamar Portland a Oregon suka fuskanci arangama da jami'an tsaro, da lalata dukiya, da ƙone-ƙone.
Duk da asali abin da ya haifar da zanga-zangar batu ne na zaluncin 'yan sanda, abin ya ta'azzara yayin da wasu ƙungiyoyi suka bayyana aƙidun ƙyamar gwamnati antida ƙyamar 'yan jari hujja.
Barazanar rikicin siyasa game da zaɓen shugaban ƙasa na 2024 ya samu ƙarfi saboda yuƙuri kashe ɗaya cikin ;yan takarar, wato Donald Trump.
Faruwar wannan abu ya dace da tsanantar adawar siyasa da yadda wasu ke neman ɗaukar mummunan mataki.
Yunƙuri kan rayuwar Trump ya zama wata hujja da ke nuna matsalar ƙaruwar haɗarin da manyan gwamnati a yanayin rarrabuwar kai da ke nuna barazanar tashin hankali bayan zaɓe.
Marubucin, Kristian Alexander Babban Mai Nazari ne kuma Daraktan International Security & Terrorism Program a Trends Research & Advisory. Ya yi aiki a matsayin ƙaramin farfesa a College of Humanities and Social Sciences at Zayed University a Abu Dhabi, a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Togaciya: Ra'ayoyin da aka bayyana a nan na marubucin ne, kuma ba sa wakiltar ra'ayi, komahangar editocin TRT Afrika.