Kamala Harris, wadda ake sa ran za ta zama ‘yar takarar shugabancin Amurka, ta daɗe tana fuskantar suka kan tarihinta mai cike da cece-kuce a matsayinta na mai gabatar da ƙara kuma babbar lauya kafin ta yi fice a siyasar Amurka.
Masu suka suna kallonta a matsayin munafuka, suna ikirarin cewa tana jin daɗin laƙabin "mai sassaucin ra'ayi" yayin da take ɗaukar matsayi mai tsauri da ke adawa da sake fasalin sassaucin ra'ayi.
A baki ɗaya rayuwarta ta aikin shari'a, Harris sau da yawa tana ƙin amincewa da sake fasalin shari'a.
A matsayinta na lauyar gundumar San Francisco tsakanin 2004 da 2011 kuma daga baya a matsayin babbar lauyar gwamnati, ko dai ta yi adawa ko kuma ta yi shiru kan sauye-sauyen da aka yi, wanda ya haifar da damuwa tsakanin masu ci gaba.
Musamman ma, ta "kafe kai da fata" don tabbatar da hukuncin ba daidai ba duk da hujjar rashin ɗa'a a hukumance, gami da lalata hujjoji da shaidar ƙarya daga masu gabatar da ƙara.
A cikin shekarar 2010, Harris ta fuskanci zargi don hana bayanai game da wani ƙwararren ɗan sanda da ake zargi da yin zagon ƙasa da satar ƙwayoyi.
Wata sanarwa ta bayyana cewa ofishinta ya san da rashin ɗa'ar ma'aikacin amma ya kasa sanar da lauyoyin tsaro, lamarin da ya sa alkali ya yi Allah wadai da Harris saboda keta hakki na tsarin mulki.
Harris ta ƙi amincewa da hukuncin, tana mai yin nuni da wani rikici da ya ci karo da muradunta saboda matsayin mijin alƙaliyar a bainar jama'a game da bayyana shaida.
Ba ta yi nasara ba a shari’ar, wadda ta yi sanadin korar shari’o’i sama da 600 da ma’aikacin mai cin hanci da rashawa ya gudanar.
Har ila yau Harris ta goyi bayan dokar jihar da ta nemi hukunta iyayen yaran da suka tsallake makarantar firamare da laifi.
Dokar ta yi tasiri sosai a kan baƙaƙen fata masu ƙarancin kuɗi, waɗanda galibi ba su da wadata da albarkatu don tabbatar da yaransu suna zuwa makaranta a duk shekara.
A shekarar 2014, Haris ta ƙi bayyana matsayarta a kan ƙuri'ar da aka kaɗa a kan dokar Proposition 47, wadda aka yi domin mayar da wasu manyan laifuka su zama ƙanana a hukumance domin rage ƙarfin hukuncinsu, sannan ta kwashe da dariya a lokacin da aka tambaye ta ƙarin bayani a game da goyon bayanta ga shan tabar wiwi domin nishadi.
Ta kuma ƙi amincewa da wani ƙudurin da aka yi domin ofishinta ya binciki wasu harbe-harben 'yan sanda, da tsarin ba 'yan sanda 'yancin amfani da ɓoyayyun kyamarori na jikinsu, waɗanda waɗannan abubuwan suka jawo mata suka daga masu yunƙurin kawo sauyi, ciki har da lauyoyin ACLU da San Francisco.
Yadda Haris ta goyi bayan wasu hukunce-hukunce suna daga hankali. A shekarar 2015, ofishinta ya amince tare da kare hukuncin da ake yanke wa George Gage -wani mai gyara wuta wanda ba a taɓa kamawa da wani laifi ba a baya - da laifin cin zarafin jikarsa.
Duk da cewa an gano yadda mai gabatar da ƙara ya ɓoye wasu shaidu, amma ofishin Haris ya ce Gage bai kawo ƙwararan hujjoji ba a ƙaramar kotu.
Alkalin Kotun Daukakar Karar ya aika ƙarar zuwa ofishin Haris domin neman shawara, amma ta ƙi yin watsi da shari'ar, wanda hakan ya tabbatar ma Gage da zaman gidan yari na shekara 70.
Haka kuma Haris ta taimaka wajen cigaba da zaman Daniel Larsen a gidan yari duk da cewa hujjoji sun bayyana gaskiyarsa, amma aka yi amfani da wasu hanyoyi aka lauya shari'ar domin tabbatar da ɗaurinsa.
A tuhumar da aka yi wa Johnny Baca, ta yi amfani da shaidun ƙarya wajen tabbatar da hukuncinsa.
A game da hukuncin Kevin Cooper, da farko ta ƙi amincewa a yi gwajin DNA domin ɗage masa hukuncin kisa, duk da cewa daga baya ta amince bayan jaridar New York Times ta fallasa yunƙurinta.
Masu suka suna ganin aikin Haris a matsayin babbar mai ƙarar da ta fi mayar da hankali a kan hanyoyin lauya shaidu domin samun hukunci sama da tabbatar da adalci.
Aikinta a ɓangaren shari'a ya sha bamban da yadda ake ganinta a zahiri na mai sauƙin kai, wadda take a shirye wajen ƙwato 'yancin baƙaƙen fata da sauran ƙananan ƙabilu.
A wannan ɗan tsakanin dai, kimanin shekara goma da suka gabata, Haris ta fito fili ta bayyana goyon bayanta a kan 'yan sanda su riƙa amfani da ɓoyayyun kyamarori, inda ta nuna cewa kowane bangaren 'yan sanda yana da 'yancin tsara yadda zai rika nadar bidiyo, da tsawon da zai dauka a hannunsu da kuma yadda za su iya fitar da shi.