Bayan da sojojin Isra'ila suka kai hari wani sansanin 'yan gudun hijira a Rafah ranar 26 ga watan Mayu har suka kashe aƙalla mutum 45, Shugaban Amurka Joe Biden ya ƙi yin Allah wadai da lamarin.
Musamman ma, shi ba ya ɗaukar kashe mata da yara da jarirai da ake yi a wani abu - duk da cewa hakan na harzuƙa al'ummar duniya - shi a ganinsa bai kai mizanin da za a ce an wuce gona da iri ba.
Kwanaki kaɗan bayan hakan, ranar 31 ga watan Mayu, sai ya shaida wa manema labarai cewa "yanzu lokaci ya yi da za a kawo ƙrshen yaƙin".
Ilai kuwa sai ga shi ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa an bai wa wata tawagar sasantawa umarnin "samar da wani tsari don cimma wannan muradin", da sharaɗin sakin mutanen da Hamas ke garkuwa da su.
Amma kuma sai ga shi a ranar Asabar, 1 ga watan Yuni, Netanyahu ya ce "ba za a cim ma wata yarjejeniyar dindindin ta tsagaita wuta ba," kuma "sharuɗɗan Isra'ila na kawo ƙarshen yaƙin ba su sauya ba."
Ya lissafa waɗannan sharuɗɗan a matsayin "lalata rundunar sojin Hamas, da sakin dukkan waɗanda ake garkuwa da su da kuma tabbatar da cewa Gaza ta daina zame wa Isra'ila barazana," yana mai bayyana cewa Isra'ila ba za ta yarda da batun tsagaita wuta na dindindin ba har sai an cika waɗannan sharuɗɗan.
Kazalika, daga baya wani mataimakin Netanyahu ya shaida wa manema labarai cewa Isra'ila ta amince da shirin Biden. Sai dai babu wata sanarwa a hukumance da ke fayyace abin da ke faruwa.
Rashin kataɓus din Isra'ila da rashin ba da amsa kan 'Shirin Biden', duk da ikirarin Shugaban Amurkan cewa tuni Tel Aviv ta ba ta umarnin, ya bijiro da tambayoyi kan ko dai da gangan Washington ke jawo ruɗani a kan shirin nata na yadda za ta kawo ƙarshen yaƙin.
Saɓanin ra'ayi
Da gayya Joe Biden, wanda ya ayyana kansa a matsayin mai tsananin son kafa ƙasar Isra'ila, ya sanar da shawararsa a daidai lokacin fara hutun Sabbath na Yahudanci - mai yiwuwa da zummar sayen lokaci, kamar yadda wani malamin jami'a Balasɗine kuma ɗan Birtaniya sannan mai fafutukar siyasa Azzam Tamimi ya faɗa.
Ta hanyar yin hakan, kafafen watsa labarai za su mayar da hankali a kan batun shawarar tasa aƙalla awa 24 kafin Isra'ila ta iya mayar da martani
Wataƙila kuma sanarwar da aka yi ranar Juma'a da marece, 31 ga watan Mayun, ka iya zama da niyyar neman goyon bayan al'ummar Isra'ilu da ba ruwansu da addini ne - waɗanda ba sa faye yin bikin hutun Sabbath ba - da niyyar hura wa gwamnatin Isra'ila wuta da aiwatar da shi, in ji Alon Liel, tsohon darakta janar na ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila, a hirarsa da TRT World.
Mambobin Majalisar Dokokin Sira'ila ta Knesset masu tsattsauran ra'ayi suna matsa wa Netanyahu lamba kan kada ya amince da duk wata yarjejeniya da Hamas, kuma kada a sassauta kai wa Gaza hare-hare, ko da bayan an saki wadanda aka yi garkuwa da su.
Wannan shi ne dalilin da ya sa 'yan siyasa masu tsattsauran ra'ayi ke jawo babban cikas ba kawai ga siyasar Netanyahu ba har ma ga Biden, in ji masana.
A lokaci guda kuma, ga alama wannan shawara ta Biden ta zo wa Netanyahu da gamayyarsa ta masu tsaurin ra'ayi a ba-zata, kamar yadda Tamimi ya gaya wa TRT World.
Yayin da ake ganin ya sanya wa Isra'ila wani abin kunya, yana ba da shawarar cewa akwai yuwuwar Biden ya hada kai da wasu jami'an Isra'ila, masu yiwuwa masu sassaucin ra'ayi, don tilasta Netanyahu ya dauki matakin tsagaita wuta.
Masana yankin sun ba da shawarar cewa masu ra'ayin riƙau a cikin gwamnatin Netanyahu na iya kasancewa a gefe yayin da ake tsara shirin.
Idan kuwa haka ne, to tabbas Ministan Tsaron Isra'ila Ben Gvir zai kasance daya daga cikin jami'an da suka fusata. Jim kadan bayan gabatar da shirin, ya bukaci Netanyahu da kada ya sanya hannu kan "yarjejeniya rashin hankali da za ta kawo karshen yakin ba tare da rugujewar Hamas ba."
Gvir ya sake jaddada barazanarsa ta ficewa daga gwamnatin idan shirin ya gudana, inda ya sake nuna cewa Netanyahu na cikin tsaka mai wuyar kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi don tsira a siyasance.
Biden na kokarin rage matsin lamba
Biden ya dage cewa a kira sabon shirin a matsayin "shawarar Isra'ila," kuma ya sanya mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller da mai magana da yawun Cibiyar Tsaron Kasa John Kirby su bayyana cewa an bunkasa shirin ta hanyar "tsarin diflomasiyya" wanda ya shafi tawagar tsaron Amurka da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Dalilin da ya sa aka sanar da wannan "shawarar Isra'ila" a Washington shi ne don tilasta Netanyahu ya aiwatar da ita, in ji Alon Liel.
Babban abin da ke haifar da muradin Biden na tsagaita wuta a rikicin na zubar da jini ba damuwar halin jinƙai ba ne. Wannan dai shi ne karuwar matsin lamba da jama'a ke fuskanta a cikin Amurka, musamman a gabanin zaben shugaban kasar Amurka.
Ta hanyar aiwatar da wani shiri mai kama da yarjejeniyoyin da aka cimma a baya wanda Hamas ta amince da su, shugaban na Amurka yana kokarin rage matsin lamba a cikin gida yayin da zabe ke ƙara kusantowa, in ji Tamimi.
A duk tsawon lokacin, Gwamnatin Biden ta aika saƙonni masu cin karo da juna, ta kasa yin matsin lamba kan Isra'ila, in ji shi.