Dadadden mai adawa da Kevin McCarthy, dan majalisa Matt Gaetz ne ya gabatar da kudurin tsige "shugaban majalisa daga kujerarsa"./Hoto: AP

An tsige kakakin majalisar wakilan Amurka Kevin McCarthy daga kan mukaminsa bayan 'yan jam'iyyar Democrats sun sanar cewa ba za su iya kubutar da shi daga hannun masu ra'ayin rikau na jam'iyyarsa ta Republican da suka sha alwashin raba shi da aikinsa ba.

'Yan majalisa na jam'iyyar Republican da ke da kaifin ra'ayi ne suka cire McCarthy daga mukaminsa ranar Tatala saboda fushin da suke yi da shi bisa hada kai da 'yan jam'iyyar Democrats.

A karon farko a tarihinta na shekara 234, majalisar wakilan Amurka ta "cire shugaban majalisa daga ofishinsa" inda masu goyon baya suke da kuri'a 216 yayin da masu adawa suka samu kuri'a 210.

An nada dan majalisa Patrick McHenry daga Arewacin Carolina a matsayin shugaban majalisar wakilai na rikon kwarya bayan tsige McCarthy.

McCarthy ya jawo zazzafar muhawara a karshen makon jiya tsakanin masu ra'ayin rikau na jam'iyyar Republican bayan ya hada gwiwa da 'yan jam'iyyar Democrat domin zartar da kudurin dokar da ya hana dakatar da harkokin gudanarwar gwamnati.

Dadadden mai adawa da McCarthy, dan majalisa Matt Gaetz ne ya gabatar da kudurin tsige "shugaban majalisa daga kujerarsa" — lamarin ya tilasta wa majalisar kada kuri'ar cire shugaban majalisar.

Batun ya bar 'yan Democrat da zabi biyu -- ko dai su kubutar da shugaban majalisar wanda yake goyon bayan tsohon shugaban kasar Donald Trump (kuma sun san illar yin hakan) ko kuma su cire shi tun da da ma shi ya kaddamar da bincike da zai kai ga tsige shugaban Amurka Joe Biden.

Gabanin jefa kuri'a, Shugaban Marasa Rinjaye Hakeem Jeffries ya bukaci 'yan jam'iyyar Democrat su tsige McCarthy, yana mai caccakar 'yan majalisar dokokin da ake yi wa lakabi da "masu ra'ayin rikau na MAGA" wato masu goyon bayan shirin Trump na "Make America Great Again".

Sai dai McCarthy ya shaida wa manema labarai a ginin majalisar dokokin cewa yana da "kwarin gwiwar cewa ba za a tsige ni ba". Daga bisani dai 'yan majalisar sun tumbuke shi daga mukaminsa shekara guda kafin babban zaben Amurka.

TRT Afrika da abokan hulda