Arevalo, ɗan shugaban kasar na farko da aka zaba a kan mulkin dimokuradiyya, Juan Jose Arevalo, ya soki yadda 'yan siyasar da aka samu da cin-hanci suke son zama shugaban kasar.  / Hoto: AFP

A wani mataki da ake yi wa kallo a matsayin mai ban mamaki, 'yan kasar Guatemala sun zabi sabon-shiga a harkokin siyasa Bernardo Arevalo a matsayin sabon shugaban kasar, kamar yadda alkaluman da hukumar zaben kasar TSE ta fitar na farko-farko suka nuna.

Kawo yanzu Arevalo ya lashe kashi 59 cikin kashi 95 na kuri'un da aka kirga, yayin da mai hamayya da shi Sandra Torres take bin bayansa da kashi 36.

Arevalo ya samu gagarumar nasara ce duk da cewa kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar kafin zaben ta nuna cewa ba zai kai labari ba bayan ya zo na biyu a zagayen farko na zaben da aka yi a watan Yuni.

Gabanin zaben na ranar Lahadi. masu sanya ido da kuma kawayen kasar na kasashen waje sun yi gargadi game da yiwuwar tafka magudi, bayan wani babban mai shigar da kara ya yi kokarin ganin an hana Arevalo yin takara sannan ya umarci yin samame a ofishin jam'iyyarsa da na hukumar zabe lokacin yakin neman zabe.

Hukumar zaben ta ce 'yan kasar sun fito sosai domin kada kuri'unsu a zagaye na biyu na zaben da aka yi ranar Lahadi, bayan a zagayen farko an samu kamfar masu fita jefa kuri'a.

'Yan kasar sun gaji da matsalolin da suka yi wa Guatemala katutu wadanda suka hada da matsanancin talauci da gagarumin cin-hanci da rikice-rikice, wadanda suka tilasta wa dubban mutane fita daga kasar zuwa Amurka don samun ingantacciyar rayuwa.

TRT Afrika da abokan hulda