Shugaban kasar Guillermo Lasso ya dora alhakin kisan Villavicencio a kan "kungiyoyin masu aikata lafuka"./Hoto: Reuters

An harbe dan takarar shugaban kasar Ecuador Fernando Villavicencio bayan gudanar da gangamin yakin neman zabe a birnin Quito ranar Laraba, a cewar manyan jami'ai na kasar.

Shugaban kasar Guillermo Lasso ya dora alhakin kisan Villavicencio a kan "kungiyoyin masu aikata lafuka" a wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, wanda a baya ake kira Twitter.

Ya yi alkawarin kama wadanda suka aikata kisan domin a hukunta su.

"Na yi matukar kaduwa da kuma bakin ciki bisa kashe dan takarar shugaban kasa Fernando Villavicencio," in ji shi.

"Domin tunawa da shi da kuma jajircewarsa, Ina mai tabbatar muku cewa wannan laifi ba zai wuce ba tare da an hukuta wadanda suka aikata shi ba."

Villavicencio, mai shekara 59, yana cikin manyan 'yan takara takwas da ke fafatawa a zaben da za a gudanar ranar 20 ga watan Agusta.

AFP