Zarge-zargen na da alaka da binciken da ake yi wa Trump na bai wa lauyansa Stormy Daniels $130,000 bayan ya biya wata karuwa kudin gabanin Trump ya lashe zabe/Hoto AFP

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya musanta aikata manyan laifuka bayan an gurfanar da shi a gaban kotun da ke cike da jama’a a birnin New York.

Shi ne tsohon shugaban kasar na farko da aka gurfanar a gaban kotu kan aikata manyan laifuka, lamarin da ka iya yin tarnaki ga burinsa na sake shiga Fadar White House a 2024.

Trump, mai shekara 76, ya shiga kotun da ke Manhattan ranar Talata a gaban gwamman ‘yan jarida inda a hukumance aka zarge shi da aikata manyan laifuka 34.

Daga nan ya Trump musanta aikata laifukan da aka zage shi a kansu.

Laifukan sun hada da hada baki wurin biyan wata tsohuwar karuwa yayin yakin neman zabensa na 2016, domin ta yi gum da bakinta game da masha’ar da ake zargi sun akata tare.

Gabanin bayyanarsa a kotun, tsohon shugaban na Amurka ya wallafa sako a shafin soshiyal midiya na Truth Social cewa "Abin al’ajabi – ZA SU KAMA NI."

Bayan fita daga kotun, Trump ya yi jawabi ga dimbin magoya bayansa a Mar-a-Lago inda ya jaddada cewa bai aikata laifi ba.

Ya ce: "Laifin kawai da na aikata shi ne yadda cikin rashin tsoro na kare mutuncin kasarmu daga wadanda suke so mu waragaza ta".

Ya ce zarge-zargen cike suke da siyasa.

Yadda shari’ar za ta kasance daki-daki

Za a iya kwashe wata da watanni ana gudanar da shari’ar, wacce ake gani ba za a soma ta ba sai shekara mai zuwa.

Trump ya ce zarge-zargen cike suke da siyasa/Hoto Reuters

Hakan na nufin za a iya sake gurfanar da tsohon shugaban kasar na Amurka a daidai lokacin da ake tsaka da yakin zaben shugaban kasa na watan Nuwanbar 2024 Sai dai kafin nan, ga jadawalin kotu game da shari’ar:

9 ga watan Mayu: A tsarin dokokin birnin New York law, wannan rana ce wa’adin da aka bai wa kowanne bangare da ke cikin shari’ar na gabatar da hujojinsa zai kare.

8 ga watan Yuni: A cewar dokokin birnin New York, wannan rana ce wa’adin da aka bai wa wanda ake zargi ya kare kansa zai kare.

8 ga watan Agusta: Wannan ne ranar da aka bai wa lauyoyin da ke kare Trump su gabatar da hujjojinsu kan daidaikun batutuwan da suka shafi shari’ar.

Lauyan Trump Joe Tacopina ya ce yana shirin gabatar da hujjojin da za su sa a yi watsi da shari’ar baki dayanta.

19 ga watan Satumba: Ranar da mai gabatar da kara zai yi martini game da hujjojin da aka gabatar.

4 ga watan Disamba: Alkali Juan Merchan zai yanke hukunci kan hujjojin da aka gabatar masa.

TRT World