Yayin da al'ummar Amurka suke shirin kaɗa ƙuri'a ranar Zaɓe, jami'an zaɓe suna kiran da kar a yi gaggawa yayain da ake tattara ƙuri'u a zaɓen shugaban ƙasa da ke cike da tarihi, inda kuma suka yi gargaɗin cewa zai iya ɗaukar kwanaki kafin sanin wanda ya lashe zaɓen.
'Yan Amurka ba sa zaɓen shugaban ƙasa kai-tsaye, saboda kwamitin masu zaɓe na musamman su 538 su ke yin zaɓen shugaban ƙasa.
Kowace jiha tana kaɗa ƙuri'arta ga ɗan takarar da ya samu rinjayen ƙuri'u. Manyan jihohi da ke da yawan wakilai a majalisar dokokin Amurka suna samu jinjayen ƙuri'u 538 da ake samu.
Mataimakiyar shugabar Amurka, 'yan jam'iyyar Democratic, Kamala Harris da abokin hamayyarta ɗan Republican, Donald Trump suna fafutukar cim ma adadin ƙuri'un kwamiti 270 wanda zai ba su tazarar rabin jimillar adadin, don su lashe zaben shiga fadar gwamnati da ke White House.
Amma takarar wannan shekarar na da zafi, inda kwararru ke nuni ga hatsarin samun jinkiri da rikitarwa kamar kalubalen doka kan kirga kuri'u.
Sama da mutane miliyan 82 sun jefa kuri'a kafin ranar Talata, sama da rabin kuri'un da aka jefa a zaben 2020.
Zuwa yaushe za a kammala ƙirgen?
Da misalin karfe 6:00 na yamma (2300GMT) za a rufe jefa kuri'un farko, amma idan zaben ya zama kai da kai, za a iya daukar kwanaki kafin a bayyana wanda ya yi nasara.
A 2020, kafafan watsa labarai na Amurka sun ayyana dan takarar Democratic Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zabe a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, duk da cewar an kammala jefa kuri'a a ranar Talata.
A 2016 da 2012 masu jefa kuri'a ba su jira da yawa ba.
Bayan an jefa kuri'u, jami'an zabe, zababbu ku wadanda aka nada, sai su ware tare da kirga kuri'un. Hanyoyin na bambanta daga wani yankin zuwa wani.
Jihohi da dama sun sauya dokokin zabe inda suke bayar da aika kuri'a ta hanyar sako ko jefa kuri'a a kasashen waje, tun kafin Ranar Zabe, duk da Pennsylvania da Wisconsin ba su yi irin wadannan sauye-sauye.
Dukkan su fagen daga ne da za su iya karkata ga wata jam'iyya. Yadda ba a yarda da jefa kuri'a ta hanyar aika sako ba, har sai ranar 5 ga Nuwamba a rumfar zabe, hakan zai sanya a jima ana kirgen.
Musamman idan kuri'u suka yi kusa hakan zai sanya a sake yin kirgen.
Wa yake tabbatar da ingancin kuri'un?
Maimakon jiran mahukuntan yankuna su bayyana wadanda suka yi nasara, kafafan yada labarai na Amurka na bayyana takarar duba ga abinda suka gani a yayin zabe.
Amma wannan ba abu ne a hukumance ba kuma dole ne sai an tabbatar da sahihancin kuri'un a matakin jiha, an tabbatar da kirga kowace kuri'a da aka jefa.
Lokacin da aka baiwa jihohi na amincewa da ingancin kuri'u shi ne 11 ga Disamba, kuma kowacce jiha ta nada masu zabe da za su jefa kuri'unsu ga 'yan takarar da suka yi nasara a zaben gama-gari.
Nan da 25 ga Disamba, dole ne ya zama Shugaban Majalisar Dattawa ya karbi shaidar nasarar zabe daga kowacce jiha, wadda ita ce Mataimakiyar Shugaban Kasa - Harris.
A ranar 6 ga Janairu, Majalisar Dokoki ta kirga da tabbatar da sakamakon zabe kafin a rantsar da sabon shugaban kasa a ranaar 20 ga Janairu.
Me zai iya janyo jinkiri?
Tabbatar da ingancin kuri'u tsari da ake bi kawai, amma kwararru na gargadin cewa akwai karin hatsarin samun kutse.
A kalla jami'an zabe a larduna 22 sun jefa kuri'a a 2022 don jinkirta tabbatar da ingancin kuri'u a jihohi. Kwararre a Brookings ya yi tsokacin hakan a makon da ya gabata.
Wannan kusan karin kashi 30 ne daga na 2020. A kalla jami'an zabe 35 "sun ƙi su amince da ingancin ƙuri'un da aka jefa kuma a yanzu ma za su iya sake yin haka," kamar yadda kungiyar CREW da ke Washington ta bayyana.
Idan aka samu nasarar yin kutse to za a yi tasiri kan wa'adin amincewa da kuri'u a jihohi da matakin tarayya, kungiyar ta yi gargadi.
An kara tsaurara matakan tabbatar da ingancin kuri'u tare da sanya siyasa a ciki tun bayan da Trump ya ki amince wa faduwa zabe a 2020. A shekarar 2020, annobar Covid-19 ma ta sake janyo jinkirin sanar da sakamako.
Haka nan akwai tarin ƙararraki gaban kotuna daga duka jam'iyyun gabanin Ranar Zaɓe, wanda zai iya kawo ruɗani wajen ƙidayar.