Donald Trump na Jam'iyyar Republican da kuma Kamala Harris ta Jam'iyyar Democrats sun tafka muhawara a ranar Talata. / Hoto: Reuters

A lokacin muhawararsu ta farko ta neman shugabancin Amurka a ranar Talata, ɗan takarar Jam'iyyar Republican Donald Trump ya zargi 'yar takarar Democrats wato mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da ƙin goyon bayan Isra'ila.

Sai dai Harris ta mayar da martani ta hanyar cewa ta shafe rayuwarta baki ɗaya tana goyon bayan Isra'ila.

A lokacin da aka tambaye shi kan ta yadda zai bi domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza da kuma tabbatar da sakin waɗanda ake tsare da su, sai Trump ya mayar da martani ta hanyar jaddada kalamansa na baya kan cewa da a ce shi ne shugaban ƙasa da tun farko yaƙin da ake yi a Ukraine da Gaza da ba a fara su ba.

"Ta tsani Isra'ila," in ji Trump. "Idan ta zama shugaban ƙasa, ina da yaƙinin Isra'ila za ta shuɗe a cikin shekara biyu daga yanzu."

"Ta ma kasa haɗuwa da (Firaiministan Isra'ila Benjamin) Netanyahu a lokacin da ya je majalisa domin yin muhimmin jawabi," kamar yadda ya ƙara da cewa.

"A daidai haka kuma a yadda take, ta tsani Larabawa," in ji Trump, "saboda za a tayar da dukan wurin: Larabawa, Yahudawa, Isra'ila. Isra'ila za ta rushe,"

A martanin da Harris ta mayar, ta bayyana cewa baki ɗaya "wannan ba gaskiya ba ne."

"Na shafe rayuwata ina goyon bayan Isra'ila da mutanen Isra'ila," in ji ta.

Ta bayyana cewa Isra'ila na da 'yancin kare kanta, ciki har da barazana daga Iran da ƙawayenta, amma ta ƙara da cewa yadda ƙasar za ta kare kanta shi ma abin dubawa ne.

"Haka kuma gaskiya ne akwai Falasɗinawa da dama waɗanda ba su ji ba su gani ba da aka kashe. Yara da iyaye mata. Abin da muka sani shi ne dole a kawo ƙarshen wannan yaƙin. Dole a kawo ƙarshensa. Kuma ta yadda zai kawo ƙarshe shi ne ta hanyar yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma fitar da waɗanda ake riƙe da su. Za mu ci gaba da aiki ba dare ba rana kan hakan," in ji ta.

Haka kuma ta jaddada matsayarta kan samar da tsarin ƙasashe biyu wato 'two-state solution' domin magance wannan yaƙin.

AA