Juma'a, 1 ga watan Nuwamba, 2024
1057 GMT — Akalla karin Falasdinawa 55 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila a Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 43,259, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi wa kawanya.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 101,827 sun jikkata a harin da ake ci gaba da kaiwa.
"Sojojin Isra'ila sun kashe mutum 55 tare da jikkata wasu 186 a kisan kiyashi uku da aka yi wa iyalai a cikin sa'o'i 24 da suka wuce," in ji ma'aikatar.
“Akwai mutane da dama waɗanda har yanzu suna nan a maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai sakamakon masu aikin ceto sun gaza tono su,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
0700 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa a hare-hare da ta kai da daddare a Gaza
Falasɗinawa aƙalla 47 sun mutu sannan gommai suka jikkata, galibinsu mata da yara, a wani luguden wuta da Isra'ila ta yi da daddare aa birin Deir Al Balah da sansanin Nuseirat da kuma garin Al Zawayda da ke tsakiyar Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA.
0626 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta umarci mazauna kudancin Beirut su bar yankin
Rundunar sojin Isra'ila ta umarci mazauna yankunan da ke wajen birnin Beirut su bar yankunan a yayin da take ci gaba da luguden wuta ta sama da ƙasa a ƙasar.
A wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun rundunar sojin Avichay Adraee ya yi iƙirarin cewa yankunan “suna kusa da maɓoyar mayaƙan Hezbollah, wadda rundunar sojojin Israila suke shirin far wa nan ba da jimawa ba.”
“Dole ku gaggauta barin gine-ginen da ke yankunan tare da nesanta kawunanku daga yankunan da nisan aƙalla mita 500 ( ƙafa 1,640),” in ji kakakin rundunar sojin.
2346 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 26 a sabbin hare-hare da ta kai a faɗin Gaza
Falasɗinawa aƙalla 26 ne suka mutu kana 47 suka jikkata sakamakon hare-hare ta sama da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai a faɗin yankin Gaza, a cewar wasu majiyoyi na asibiti.
Da farko, jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a wani gida da ke yankin Sabra a kudancin Birnin Gaza, inda suka kashe Falasɗinawa biyu da jikkata huɗu, in ji majiyoyin.
Kazalika, wani hari da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai kan wani taron jama'a a garin Al-Zawayda da ke yankin tsakiyar Gaza ya kashe Falasɗinawa biyu tare da jikkata mutum uku.
Bugu da ƙari, wasu hare-hare da sojojin Isra'ila suka kai a gidaje biyu da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke arewacin Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 16 da jikkata 30, ciki har da ƙananan yara.
Majiyoyin sun ƙara da cewa Falasɗinawa huɗu sun mutu sannan goma sun jikkata, ciki har da yara, a wani luguden wuta da dakarun Isra'ila suka yi a gidansu da ke arewa maso yammacin Birnin Gaza.
Sai kuma Falasɗinawa biyu 'yan'uwan juna da jiragen yaƙin Israila suka kashe tare da jikkata gomman lokacin da suka kai harin bam a wani gida da ke Deir al-Balah a tsakiyar Gaza, kamar yadda ma'aikatan kiwon lafiya suka shaida wa kamfani dillancin labarai na Anadolu Agency.
Ƙarin labarai 👇
0349 GMT — Rokokin da aka harba daga Lebanon sun kashe mutum 7 a Isra'ila ciki har da 'yan ƙasar Thailand huɗu
Rokokin da aka harba daga Lebanon zuwa arewacin Isra'ila sun kashe ma'aikata 'yan ƙasashen waje huɗu da 'yan Isra'ila uku, a cewar ma'aikatan asibitin Isra'ila, wanda shi ne hari mafi muni da aka kai wa Isra'ila tun da ta soma mamayar Lebanon.
Thailand ta tabbatar da cewa 'yan ƙasar huɗu na cikin waɗanda suka mutu sakamakon harin na rokoki.
Ministan Harkokin Wajen Thailand, Maris Sangiampongsa ya wallafa saƙo a shafinsa na X inda ya bayyana "matuƙar baƙin ciki" bisa kisan da aka yi wa 'yan ƙasarsa a kusa da garin Metula ranar Alhamis, inda ya ƙara da cewa an jikkata wani ɗan ƙasar tasu guda ɗaya.