Mutane fiye da 230 ne suka rubuta wasiƙa da ke neman BBC ta riƙa watsa labarai ba tare da nuna son-kai ba. / Hoto: Reuters

Ɗaruruwan mutane ciki har da ma'aikatan BBC sun zargi kafar watsa labaran da goyon bayan Isra'ila a rahotannin da take bayarwa game da yaƙin Gaza, inda suka yi kira a gare ta da ta "mayar da hankali wajen yin adalci da bayar da labaran gaskiya da daina nuna son-kai."

Mutane fiye da 230 sun aika wasiƙa ga Darakta Janar na BBC Tim Davie, ciki har da ma'aikatan BBC 101 da suka nemi a ɓoye sunayensu da 'yan jaridar wasu kafofin watsa labarai da masana tarihi da malaman jami'a da 'yan siyasa, a cewar wani rahoto da jaridar The Independent ta soma wallafawa ranar Juma'a.

Wasiƙar ta soki BBC bisa gazawa wajen bin ƙa'idojin aikinta na watsa labarai, ta yadda ta ƙi bayar da "sahihan rahotanni" game da yaƙin Gaza."

Kazalika wasiƙar ta yi kira ga BBC ta riƙa bayar da rahotanni "ba tare da jin tsoro ko nuna son-kai ba” da kuma "gudanar da aikin watsa labarai bisa ƙa'idoji na ainihi — cikin adalci da sahihanci da rashin nuna son-kai."

"Watsa labaran ƙarya na da mummunan tasiri. Duk wani labari na talbijin da na shafukan intanet da kuma rediyo da ya gaza ƙalubalantar iƙirarin Isra'ila, yana bin tsarin musguna wa Falasɗinawa ne kawai," a cewar wasiƙar.

Sai dai BBC ta musanta waɗannan zarge-zarge, inda ta dage cewa tana "gudanar da aikinmu na watsa labarai da aka fi amincewa da shi ba tare da nuna son-kai ba."

Wani mai magana da yawun kafar watsa labaran ya ce: "Idan muka yi kura-kurai ko muka canza yadda muke bayar da rahotanni, muna bayyanawa a fili. Kazalika muna fitowa fili mu gaya wa masu bibiyarmu tarnaƙin da muke fuskanta wajen bayar da rahotanninmu – da suka haɗa da rashin samun damar shiga Gaza da taƙaitattun wuraren da aka bari mu shiga a Lebanon, da kuma jimirin da muke ci gaba da yi wajen ganin masu aiko da rahotanninmu sun samu damar shiga waɗannan wurare."

AA