Kafar watsa labarai ta BBC ta sayar da wani katafaren dandalin shirye-shiryenta na Maida Vale Studios ga wani kamfani wanda mai shirya fim da wakar nan na kasar Jamus Hans Zimmer ke ciki masu sayen.
Katafaren dandalin na da dakunan nadar shirye-shirye bakwai. BBC ta sayi wurin wanda yake a arewa maso yammacin birnin Landan a 1933.
A tsawon shekarun da suka gabata, dakunan shirye-shiryen sun karbi bakuncin mawaka kamar su Beyonce da The Beatles haka kuma an sha yin taron mawaka masu tasowa wanda DJ John Peel ya jagoranta.
Haka kuma a wurin ne aka rinka hada kade-kade da dama inda a nan aka hada kidan wani wasa na talabijin “Doctor Who”.
Sai dai dama tuni Maida Vale Studios ya shiga cikin barazana tun bayan da BBC ta sanar a 2018 cewa bangaren zai koma karkashin BBC Music Studios wanda aka gina a gabashin Landan.
Zimmer da abokin kasuwancinsa Steve Kofsky sun hada kai da masu shirya fim Tim Bevan da Eric Fellner domin sayen wurin, in ji BBC.
Ba a bayyana kan nawa aka sayar da wurin ba, sai dai BBC din ta bayyana cewa wadanda suka sayi wurin sun yi alkawarin kashe miliyoyin daloli domin yi masa kwaskwarima.