Kafar watsa labarai ta BBC ranar Litinin ta yarda cewa ta yaudari jama'a game da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa da aka gudanar a Birtaniya a karshen mako wadda tun da farko ta bayyana a matsayin ta "goyon bayan Hamas."
"Tun da farko a labaran BBC News, mun bayar da rahoto game da wasu jerin zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a karshen mako. Mun yi magana a kan zanga-zanga da dama da aka yi a fadin Birtaniya inda mutane suka bayyana goyon bayansu ga Hamas.
"Mun amince cewa ba mu yi abin da ya kamata ba kuma mun yaudari jama'a kan zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa," a cewar babbar mai gabatar da shiri Maryam Moshiri a yayin da take gabatar da shiri kai-tsaye a BBC World News
Kazalika Moshiri ta wallafa wannan sanarwa a shafin X wanda a baya ake kira Twitter.
Tun da farko ranar Litinin, wani mai aiko da rahotanni kan ziyarar da Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak ya kai wata makarantar Yahudawa a London, ya ce ya kai ziyarar ce bayan jerin zanga-zangar da aka yi a Birtaniya inda "mutane suka bayyana goyon bayansu ga Hamas, wadda kasashe da dama, ciki har da Birtaniya da Amurka, suke kallo a matsayin ta ta'addanci."
Hakan ya sa mutane sun rika sukar kafar watsa labaran a shafukan sada zumunta inda suka bayyana ta matsayin mai nuna "son kai."
Ranar Asabar, kusan mutum 150,000 a London suka gudanar da gagarumin gangami na goyon bayan Falasdinawa.