‘Yan majalisar Scotland suna daf da tabbatar da nada Humza Yousaf ranar Talata, a matsayin sabon Shugaban gwamnati, bayan da ya cimma nasara da jibin goshi na zama magajin shugabar jam’iyyar Scottish National Party (SNP), wato Nicola Sturgeon.
Yousaf ya doke ‘yan takara biyu a jam’iayyar SNP a ranar Litinin, har ya karbe shugabancin jam’iyyar.
Ya sha alwashin farfado da sanannen kudurin jam’iyyarsu na nemo ‘yancin kai ga Scotland, wanda ya samu tsaiko cikin watannin baya-bayan nan.
Yousaf mai shekara 37 ya za zamo shugaban gwamnati mafi karancin shekaru tun bayan kirkirara majalisar Scotland a shekarar 1999.
Haka nan zai zamo mutumin da ba fari ba na farko, kuma Musulmi na farko da zai jagoranci kasa mai yawan al’umma miliyan 5.5.
“Ya kamata a yau mu yi alfahari da cewa mun isar da sako a bayyane cewa launin fata, ko addini ba zai zama tarnaki ga zama mai jagorar wannan kasa da muke kira kasarmu ba,” Yousaf ya fada bayan lashe zaben shugabancin SNP.
Ya dauki alkawarin zama shugaba ga “duka ‘yan Scotland”, kuma ya sha
“Za mu kasance karnin da zai samo mana ‘yancin kai ga Scotland,” Yousaf ya shelanta yayin gabatar da jawabin cin nasara.
‘Mayar da hankali’
Mamabobin Majalisar Scotland za su yi zabe ranar Talata don nada sabon shugaban gwamnati daidai tsakiyar rana.
Yousaf yana da tabbacin gadar Nicola Sturgeon, kasancewar SNP ita ce jam’iyya mafi girma. Daga nan za a yi bikin rantsar da shi ranar Laraba.
Wannan babban sauyi a siyasar Scotland ya biyo bayan ajiye aikin ba tsammani
Nicola Sturgeon ‘yar shekara 52, ta ce za ta ajiye aiki ne saboda tana jin ba za ta iya bayar da “cikakken karfinta” wajen gudanar da aikinta ba.
Hakan yana zuwa ne bayan tsanantar lamura a gwamnatinta, a lokacin da ta rasa goyon baya wajen neman ‘yanci.
Kuri’o’in jin ra’ayi na baya-bayan nan sun nuna cewa kusan kashi 45 cikin 100 na ‘yan Scotland suna goyon bayan kasar ta fice da Burtaniya.
Wannan kaso ya yi daidai da wanda aka samu a kuri’ar raba-gardama ta shekarar 2014, wadda gwamnatin Burtaniyan ta ayyana a matsayin wanda ya yanke hukunci kan batun ‘yancin kan scotland a wannan karni.
A ranmar Litinin Yousaf ya ambata cewa zai ci gaba da shirin Nicola Sturgeon na neman gwamnatin ‘yan mazan jiya da ke can Landan da ta nemi a sake wani zaben raba-gardama.
Gwamnatin Burtaniya ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen sukar wannan magana, inda firaminista mai magana da yawun Firaminista Rishi Sunak ya fada wa manema labarai cewa abin da ya kamaci sabuwar gwamnati ta SNF shi ne batutuwan tattalin arziki da suke da “muhimmanci” ga masu zabe a Scotland.
Takara cikin rabuwar kai
Yousaf, wanda ya kasance ministan lafiya a gwamnatin Nicola Strugeon ta karshe, ya sha da kyar wajen zama sgugaban SNF, inda ya samu kashi 52 cikin 100 na kuri’u.
Duk da a karshe ya cimma nasara, Yousaf ya sha suka kan iya aikinsa yayin da ya rike mukamai daban-daban a gwamnati.
Yanzu zai fuskanci babban kalubale kafin samun amincewar jama’ar Scotland masu zabe, yayin da babban zaben Burtaniya ke karatowa cikin wata 18 masu zuwa.
A cewar shirin jin ra’ayi na Ipsos, kashi 22 na masu zabe suna yabon Yousaf.
Duk da cewa jam’iyyar SNP ta yi ta cin zabe a lokacin gwamnatin Nicola