1652 GMT — Gwamnatin Isra'ila ta ayyana "yanayi na musamman" dokar ta-ɓaci a duka faɗin ƙasar, har zuwa 30 ga watan Satumba.
1431 GMT — Akalla mutane 274 da suka hada da yara 21 da mata 31 ne suka mutu yayin da wasu 1,024 suka jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon, in ji ministan lafiya na kasar yayin wani taron manema labarai.
1158 GMT — Isra'ila na shirin kai manyan hare-hare a Beqaa na Lebanon - Sojoji
Jiragen saman Isra'ila na shirin kai hari kan katafaren wajen da ake ajiye da manyan makamai na kungiyar Hizbullah a yankin Beqaa na kasar Lebanon, in ji kakakin rundunar sojin Isra'ila, inda ya yi kira ga fararen hula da su gaggauta ficewa.
"Abin da ake gani a kudancin kasar Lebanon, shi ne fashewa ta biyu na makaman Hizbullah, wadanda ke tashi a cikin gidaje. A duk gidan da muke kai hari akwai makamai. Roka, makamai masu linzami, jiragen sama marasa matuka wadanda aka yi d nufin kashe fararen hula na Isra'ila," Rear Admiral Daniel Hagari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin.
0700 GMT — Isra'ila ta kashe yara biyar da mata biyu a wani sabon harin da ta kai Gaza
Aƙalla Falasɗinawa takwas waɗanda suka haɗa da mata biyu da yara biyar Isra'la ta kashe a wani sabon hari ta sama da ta kai wata makaranta ɗauke da farar hula a tsakiyar Gaza.
An kashe wata uwa da 'ya'yanta huɗu haka kuma an jikkata wasu a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai gidan iyalin Al-Samak da ke birnin Deir al Balah, kamar yadda hukumar kare farar hula ta Gaza ta tabbatar.
A wata sanarwa ta daban, hukumar kare farar hulan ta kara da cewa harin da Isra'ila ta kai kan makarantar Khaled Bin Al-Waleed da ke sansanin 'yan gudun hijira na Al-Nuseirat, ya kashe wani mutum, matarsa, da 'yarsu, tare da jikkata wasu.
0630 GMT — Gomman hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama a kudanci da gabashin Lebanon sun yi sanadin mutuwar aƙalla farar hula ɗaya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NNA ya tabbatar.
“Jiragen yaƙin maƙiya sun ƙaddamar da hare-hare....sama da hare-hare 80 a cikin minti 30”, inda suka afka gundumar Nabatiyeh da ke kudancin Lebanon,” in ji kamfanin dillancin labaran na Lebanon.
Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare tsakanin mayaƙan Hezbollah na Lebanon da kuma sojojin Isra’ila.