Sojojin juyin juya halin Iran sun ce sun kai hari da makami mai linzami kan hedikwatar ofishin leken asirin Isra’ila na Mossad da ke Iraki da Syria, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito.
“Rundunar Juyin Juya Hali ta Musulunci ta sanar da lalata hedikwatar leken asiri da tattara bayanai na kin jinin Iran [Mossad] a sassan yankunan da makamai masu linzami,” kamar yadda kafar watsa labarai ta IRNA ta ruwaito a ranar Talata.
“Wannan hedikwatar ta kasance wata cibiya ta leken asiri da kuma shirya hare-haren ta’addanci a yankin,” in ji ta. Kafar watsa labarai ta Fars ta ruwaito cewa an lalata hedikwatar Mossad ta Isra’ila a yankin Kurdawa na Iraki.
Sannan kuma an kashe farar hula akalla hudu da kuma raunata shida a wani hari da aka kai a Erbil, kamar yadda Majalisar Tsaro ta Gwamnatin Yankin Kurdawa ta bayyana a wata sanarwa inda ta bayyana harin a matsayin “laifi”.
Haka kuma sojojin juyin juya halin sun kaddamar da harin makami mai linzami kan wuraren “’yan ta’adda” da ke Syria domin mayar da martani kan tagwayen bama-bamai na kunar bakin wake da aka yi a Iran a wata nan wadanda kungiyar ta'addanci ta Daesh ta dauki nauyin kaiwa, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar ta ruwaito.
Duka sansanonin sojin Amurka na cikin aminci
Hare-haren makamai masu linzami a Iraki ba su taba wani wuri na Amurka ba haka kuma babu wani dan Amurka da ya jikkata, kamar yadda wasu jami’an Amurka biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Sai dai sojojin kasar ba su yarda sun yi karin bayani ba kan wannan lamarin. An ji karar fashewa a wani wuri wanda yake da nisan kilomita 40 daga arewa maso gabashin Erbil a yankin da Kurdawa ke da iko da shi, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
Sun ce wurin yana kusa da wani karamin ofishin jakadancin Amurka haka kuma akwai gidajen farar hula a kusa. Tun can dama ana zaman doya da manja tsakanin Iran da Amurka tun kafin a soma yaki tsakanin Isra’ila da Gaza.