1952 GMT ––Hezbollah ta ƙaddamar da hare-hare na rokoki zuwa arewacin Isra'ila
Gidan rediyon rundunar sojin Isra'ila ya ruwaito cewa an harba rokokin ne zuwa yankin Yammacin Galilee.
Wannan shi ne hari na farko da ƙungiyar ta kai tun bayan da mahukunta a Tel Aviv suka kashe shugaban Hezbollah Fouad Shukr ranar Talata a Beirut.
An kashe aƙalla mutum bakwai, ciki har da yara biyu, a harin da Isra'ila ta kai ta sama, a cewar hukumomi a Lebanon.
1005 GMT –– Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla huɗu tare da jikkata da dama a wani hari ta sama da ta kai a tsakiyar Gaza, a cewar ma'aikatan lafiya.
Lamarin ya faru ne yayin da jirin yaƙin Isra'ila ya kai hari kan wasu fararen-hula a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat, in ji ganau.
Likitoci a Asibitin Al-Awda sun tabbatar da cewa an kai musu gawawwakin mutum huɗu bayan Isra'ila ta kashe su a harin da ta kai musu.
0840 GMT — Isra'ila ta yi iƙirarin kashe kwamandan Hamas Mohammed Deif a Gaza
Rundunar sojojin Isra'ila ta yi iƙirarin kashe shugaban ɓangaren soji na Hamas, Mohammed Deif, a harin da ta kai ta sama a Gaza a watan Yuli.
Isra'ila ta kai harin ne ranar 13 ga watan Yuli a wani gida a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza inda ta kashe Deif, ko da yake ba a tabbatar da kisansa ba a wancan lokacin.
Kazalika Isra'ila ta kashe Falasɗinawa sama da 90, ciki har da fararen-hula 'yan gudun hijira da ke zaune a wasu tantuna a wancan lokacin, a cewar ma'aikatar kiwon lafita ta Gaza.
0444 GMT — An soma jana'izar shugaban Hamas Ismail Haniyeh
An soma gudanar da jana'izar shugaban ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Iran, bayan Isra'ila ta yi masa kisan gilla a gidansa da ke Tehran.
Shugaban Addini na Iran Ali Khamenei ne yake jagorantar sallar jana'izar Haniyeh amma daga bisani za a kai gawarsa Doha domin a binne ta. Tun da farko Khamenei ya yi barazanar "ɗaukar hukunci mai tsauri" kan kisan.
A tsakiyar babban birnin Iran, dubban mutane ne suka riƙe hotuna da kwalaye masu ɗauke da sunana Haniyeh da tutocin Falasɗinu inda suka taru a Jami'ar Tehran University da sanyin safiyar Aalhamis, a cewar wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP.
Rundunar zaratan sojojin Iran ta Revolutionary Guard ta sanar da kisan gillar da Isra'ila ta yi wa Haniyeh da mai tsaron lafiyarsa a harin da ta kai ta sama a gidansa da ke Tehran da tsakar daren Laraba.
0056 GMT — Jagoran addini na Iran Khamenei ne zai jagoranci jana'izar Ismail Haniye na Hamas
Tashar talabijin ta ƙasar Iran Presstv ta ce Jagoran addinin Musulunci na kasar Ali Khamenei zai jagoranci sallar jana'izar shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, kana kuma jagoran tattaunawar zaman lafiya Ismail Haniyeh.
Tashar talabijin ta Press TV ta ƙara da cewa, za a gudanar da jana'izar ne a Tehran babban birnin kasar Iran.
Da sanyin safiyar Laraba ne Isra’ila ta kashe Haniyeh a birnin Tehran, harin da ya janyo barazanar daukar fansa kan Isra’ila tare da ƙara nuna fargabar cewa yaƙin kisan kare dangi na Tel Aviv a Gaza yana rikidewa zuwa yaɗuwa a yankin Gabas ta Tsakiya.
2211 GMT — Kwamitin Tsaro na MDD ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas
Wakilan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da kisan gillar da Isra'ila aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Tehran babban birnin kasar Iran, yayin da wakilan dindindin na Amurka da Birtaniya suka zargi Iran da tada zaune tsaye a yankin.
Kwamitin ya kira wani zama na gaggawa kan kisan Haniyeh bisa bukatar Iran, wadda ke samun goyon bayan Rasha da Aljeriya da China.
Da yake jawabi a wajen taron, jakadan kasar China Fu Cong ya ce, kasarsa ta yi kakkausar suka ga kisan gillar da aka yi wa Haniyeh.
Yayin da ya kira lamarin "yunkuri na neman kawo cikas ga kokarin samar da zaman lafiya," Cong ya jaddada cewa, "China ta damu matuka game da kara ta'azzara tarzoma a yankin da wannan lamari zai iya haifar da shi."
Hakazalika wakilin Aljeriya a Majalisar Dinkin Duniya Amar Bendjama ya ce: "Muna kan hanyar ganin bala'i," ya kara da cewa harin na Isra'ila "aikin ta'addanci ne" wanda ya saɓa wa dokokin kasa da kasa da kuma ikon Iran.
"Wannan ba wai hari ne kawai kan mutum daya ba, wani mummunan hari ne kan tushen dangantakar diflomasiyya, da tsarkin mulkin kasa da kuma ka'idojin da ke tafiyar da tsarinmu na duniya," in ji shi.