Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya zargi Saudiyya da cin amanar Falasdinawa ta hanyar neman daidata alakarta da Isra'ila.
"Dabbaka dangantaka tsakanin gwamnati mai kaifin kishin Yahudanci da duk wata kasa a yankin nan, idan dai da nufin samar da tsaro ne ga gwamnatin Yahudawa, to tabbas ba za ta yi hakan ba," Raisi ya shaida wa taron manema labarai a ranar Laraba yayin da ya halarci Babban Taron MDD.
"Mun yi amannar cewa dangantaka tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da gwamnatin Yahudawa zai zama tamkar cin dunduniyar al'ummar Falasdinawa ce da kuma jajircewarsu," ya ce.
A baya Saudiyya da Isra'ila suna da manufa daya ta adawa da Iran, duk da cewa Riyadh ta yi kokarin sassauta matsalar da ke tsakaninta da Tehran ta hanyar shiga tsakanin China.
Wani labarin mai alaka: An dakatar da Ministar Harkokin Wajen Libya bayan ta gana da takwaranta na Isra'ila
Batun Falasdinu
Martanin Iran na zuwa ne bayan da Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya Mohammed bin Salman ya ce yarjejeniyar sasanci da Amurka ta samar na ci gaba da gudana don daidata alakar kasarsa da Isra'ila, a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta Fox News.
"Muna sake samun kusanci a kowace rana," in ji Mohammed bin Salman, wanda aka fi sani da MBS.
"Batun Falasdinu yana da matukar muhimmanci a wajenmu. Muna bukatar warware wannan matsalar," a cewar MBS lokacin da aka tambaye shi kan ko me ake bukata don cimma yarjejeniyar kyautata alakar.
"Kuma har zuwa yanzu muna samun kyakkyawar fahimta ta sasantawa."
Kasashen Larabawa kadan ne suke da dangantakar diflomasiyya da Isra'ila.
Masar da Jordan ne kasashe na farko da suka fara kulla alaka da Isra'ila ta hanyar kulla yarjejeniya daban-daban a shekarar 1979 da 1991.
A shekarar 2020, a wata yarjejeniya ta Abraham Accords, wasu kasashen hudu sun gyara alakarsu da Isra'ila, ciki har da Maroko da Hadaddiyar Daular Larabawa UAE da kuma Sudan.