Turkiyya ta dade tana matsa lamba ga Amurka domin Isra'ila ta tsagaita wuta a hare-haren da take kai wa Falasdinawan Gaza. / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan sun karbi bakuncin Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yakin Gaza da batun neman amincewar Turkiyya don Sweden ta shiga kungiyar NATO da kuma neman amincewar Majalisar Dokokin Amurka domin a sayar wa Turkiyya jiragen yakin F-16.

Ganawar da suka yi ranar Asabar a gidan shugaban kasa na Vahdettin ta samu halartar shugaban Hukumar Leken Asirin Turkiyya (MIT) Ibrahim Kalin da Jakadan Amurka ta Jeffry Flake.

Tun da farko, Blinken da Ministan Wajen Turkiyya Hakan Fidan sun gana a kebe.

"A yayin ganawar tasu, Ministocin sun tattauna game da yakin Gaza da kai kayan agaji, da neman amincewar Turkiyya domin Sweden ta shiga kungiyar tsaro ta NATO da batutuwan da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu," in ji Ma'aikatar Wajen Turkiyya a sakon da ta wallafa a shafin X.

Lokacin ganawar tasu, Ministan Wajen Turkiyya Fidan ya jaddada bukatar kammala sayar musu da jiragen yaki na F-16, yana mai cewa Majalisar Dokokin Turkiyya ce take da alhakin amincewa domin Sweden ta shiga kungiyar NATO, a cewar wasu majiyoyin diflomasiyya na Turkiyya.

A tattaunawar da suka yi a kan halin da ake ciki a Gaza, majiyoyin sun ambato Minista Fidan ya bayyana cewa hare-haren daIsra'ila ke ci gaba da kai wa babbar barazana ce ga yankin.

Ya nuna buktar tsagaita wuta cikin gaggawa da shigar da kayan agaji Gaza, yana mai jaddada cewa dole a samar da kasashe biyu masu 'yancin kansu idan aka son zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Minista Fidan, yayin da yake bayyana aniyarsu ta kauce wa tayar da jijiyoyin wuya game da batun Bahar Aswad, ya kuma jaddada cewa Turkiyya za ta tabbatar da tsarin raba hatsi da ke fitowa daga Rasha da Ukraine ga kasashen duniya ba tare da nuna wariya ba, kamar yadda majiyar ta kara da cewa.

Kazalika sun tattauna kan batutuwan da suka shafi yankin, ciki har da batun Azerbaijan da Armenia da halin da ake ciki a Syria da Iraki.

TRT World