1233 GMT — Ƴan sandan Faransa sun toshe ofishin jakadancin Iran da ke Paris: Majiyoyin tsaro
Ƴan sandan Faransa sun toshe ƙaramin ofishin jakadancin Iran da ke Paris kuma suna shirin shiga cikinsa idan suka samu izini, bayan wasu rahotanni sun ce wani ya je wurin da abin da ke fashewa, a cewar wata majiya daga rundunar ƴan sanda.
"Wani da ya ga abin da ya faru ya ce wani mutum ya shiga ofishin ɗauke da gurneti ko kuma ɗamarar da ke shafewa," in ji majiyar, inda ya ƙara da cewa an tura zaratan ƴan sanda ofishin jakadancin bayan da jami'ansa suka buƙaci hakan.
Wani wakilin kamfanin dillancin labaria na AFP ya ce an yi ƙawanya ga dukkan yankin da ke kusa da ƙaramin ofishin jakadancin ba wanda yake yanki na 16 kuma an jibge jami'an tsaro.
A wani saƙo da hukumar sufuri ta Paris RATP ta wallafa a shafinta na X, ta ce an dakatar da zirga-zirga a hanyoyi biyu da ke zuwa ƙaramin ofishin jakadancin.
Jami'an tsaron Faransa sun tsare mutumin da ke ɗauke da abubuwan fashewar.
0448 GMT — Filayen jiragen saman Tehran sun ci gaba da aiki: Kamfanin labaran Iran
Kamfanin dillancin labaran Iran ya ce filayen jiragen sama biyu na Tehran sun koma bakin aiki bayan da suka dakatar da aiki sakamakon ƙarar fashewar abubuwa da aka ji a tsakiyar Iran.
"Jirage sun ci gaba da zirga-zirga a filayen Imam Khomeini da Mehrabad," a cewar kamfanin dillancin labarai na IRNA.

0424 GMT — Isra'ila ta umarci ofisoshin jakadancinta su yi gum da bakinsu kan harin da ta kai wa Iran
Hukumomin Isra'ila sun umarci ofisoshin jakadancin da ke faɗin duniya su guje wa yin tsokaci game da harin da suka kai wa Iran, a cewar kafar watsa labarai ta Channel 12.
0304 GMT — Kafofin watsa labaran Iran sun ce babu abin da ya sami tashoshin nukiliyar Isfahan
Kafafen watsa labaran Iran sun ce tashoshin nukiliya da ke kusa da birnin Isfahan na tsakiyar ƙasar suna "cikin tsaro" bayana an ji ƙarar fashewa a kusa da yankin da suke.
"Tashoshin nukiliya da ke lardin Isfahan suna cikin tsaro," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito ina ya ambato wasu "sahihan majiyoyi".
0050 GMT — Iran ta musanta iƙirarin kai mata harin 'makamai masu linzami', ta ce ta lalata jirage 3 maras matuƙa na Isra'ila
Wani jami'in gwamnatin Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa babu wani harin makamai masu linzami da aka kai a cikin ƙasarsu, yana mai ƙaryata rahotannin kafafen watsa labaran Amurka da ke cewa Isra'ila ta kai musu hari.
An ambato kakakin hukumar kula da sararin samaniyar Iran yana cewa ba a kai musu harin makamai masu linzami ba, inda ya ƙara da cewa na'urorinsu sun kakkaɓo jirage maras matuƙa da dama daga sararin samaniyar yankin Isfahan.
Sai dai jami'an gwamnatin Amurka biyu sun tabbatar wa CBS News cewa wani makami mai linzami na Isra'ila ya sauka a Iran. Reuters ya ruwaito cewa Isra'ila ta gaya wa Amurka shirinta na kai wa Iran hari.
Wasu jami'an gwamnatin Amurka da ba sa so a ambace su sun shaida wa CBS News cewa Isra'ila ta yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango a harin da ta kai wa Iran.
Wani jami'in Amurka ya shaida wa CNN cewa mahukunta a Washington ba su "amince" Isra'ila ta kai harin ba.
"Ba mu amince a mayar da martani ba," a cewar jami'in gwamnatin Amurka. Jami'in ya tabbatar da cewa Isra'ila ta shaida wa Amurka cewa za ta kai wa Iran hari nan da kwanaki masu zuwa.

0040 GMT — Isra'ila ta kai wa Iran harin makamai masu linzami
Isra'ila ta kai wa Iran harin makamai masu linzami, in ji ABC News, wanda ya ambato jami'an gwamnatin Amurka.
Kazalika kamfanin dillancin labarai na Fars news da ke Iran ya bayar da rahotannin fashewar wasu abubuwa a filin jirgin saman tsakiyar Isfahan, ko da yake ba a san dalilin aukuwar fashewar ba.
"Har yanzu ba a san dalilin aukuwar fashewar ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da musabbabin wannan lamari," in ji Fars news Agency. An soma juya akalar jiragen fasinja ranar Juma'a da safe a yammacin Iran, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.
A ƙarshen makon jiya, Iran ta ƙaddamar da jerin hare-hare na ɗaruruwan makamai masu linzami da jirage maras matuƙa a Isra'ila don yin raddi kan harin da Isra'ila ta kai ƙaramin ofishin jakadancinta da ke Syria.
A birnin Isfahan ne ake da manyan filayen jiragen saman sojin Iran, da kuma tashoshin nukiliyarta. Jami'an gwamnatin Iran ba su bayar da martani ba kawo yanzu. Isfahan na da nisan kilomita 350 daga Tehran, babban birnin Iran.

2240 GMT — Amurka da Birtaniya sun sanar da sanya wa Iran jerin takunkumai kan harin da ta kai wa Isra'ila
Amurka da Birtaniya sun sanar da sanya wa Iran jerin takunkumai a fannin jirage maras matuƙa na sojinta sakamakon harin da ta kai wa Isra'ila da makamai masu linzami da jirage maras matuƙa a ƙarshen mako.
"A yau, za mu ɗauki mataki kan Iran — za mu sanya mata sabbin takunkumai da taƙaita abubuwan da za ta fitar ƙasashen waje," a cewar shugaban Amurka Joe Biden a wata sanarwa da ya fitar.
"Harin da gwamnatin Iran ta kai wa Isra'ila na ganganci ne kuma yana da hatsari na watsuwar rikici," in ji Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak, inda ya ƙara da cewa Birtaniya ta sanya takunkumai kan "shugabannin sojoji da rundunonin tsaron Iran waɗanda suke da nauyin kai harin ƙarshen mako."
Iran ta ƙaddamar da hari kai-tsaye karon farko zuwa cikin Isra'ila ranar Asabar domin yin martani kan harin da Isra'ila ta kai a ofishin jakadancinta da ke Damascus ranar 1 ga watan Afrilu inda ta kashe zaratan sojojin runduna ta musamman ta Islamic Revolutionary Guard Corps, ciki har da janar guda biyu.