Litinin, 7 ga watan Oktoba, 2024
1447 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarun tsaron sama sun dakile wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen a daidai lokacin da ake tunawa da harin na ranar 7 ga watan Oktoba.
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce, an harba makami mai linzami daga kasar Yemen, inda a baya kungiyar da ke samun goyon bayan Iran ta harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila, a cewar sanarwar da sojojin suka yi, tare da jin karar gargadi a cibiyar kasuwanci ta Tel Aviv.
1006 GMT — Adadin wadanda suka mutu sakamakon yaƙin Isra'ila a Gaza ya haura 41,900
Akalla Falasdinawa 39 aka kashe a hare-haren Isra’ila a Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bayan da Tel Aviv ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a bara zuwa 41,909, in ji ma’aikatar lafiya a yankin.
Sanarwar ma'aikatar ta kara da cewa wasu mutane 97,303 ne suka jikkata a harin.
Ma'aikatar ta ce: Sojojin Isra'ila sun kashe mutane 39 tare da raunata wasu 137 a kisan gilla da aka yi wa iyalai hudu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
0825 GMT — Hamas ta harba wa Isra'ila rokoki don tunawa da ranar 7 ga Oktoba
Ƙungiyar Hamas da ke Gaza ta harba rokoki huɗu a cikin Isra'ila a ranar cika shekara guda da ta ƙaddamar da harin Operation al-Aqsa Flood na ranar 7 ga watan Oktoban bara.
Ƙungiyar gwagwarmayar ta Falasɗinawa, Hamas, ta ɗauki nauyin hare-haren rokoki da aka nufi Tel Aviv, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta ce ta kai hari kan dakarun Isra'ila a yankuna da dama da ke Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta tare rokoki uku da yayin da na huɗu ya faɗa a wani wuri da babu mutane.
Babu rahoton mutuwa ko jikkata sakamakon harba rokokin.
A nata martanin, Isra'ila ta kai hare-hare da makaman atilari da hare-hare ta sama da tsadar dare zuwa safiyar Litinin domin daƙile abin da ta kira yiwuwar kai mata hari.
0118 GMT — Isra'ila tana ci gaba da kai hare-hare a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe shekara guda tana kai wa a Gaza sun haddasa asarar rayuka da ta gine-gine.
Sojojin Isa'ila sun kai hare-hare na kisan ƙare-dangi kusan 3,650 a shekara ɗaya da ta gabata, a cewar alƙaluman da ofishin watsa labara na Falasɗinu da ke Gaza ya fitar.
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 41,800 tare da jikkata mutum fiye da 96,800, baya ga aƙalla mutum 10,000 da suka ɓata ko kuma ake tsammani suna danne a ƙarƙashin ɓaraguzai
An gano gawawwakin Falasɗinawa 520 daga wasu manyan ƙaburbura bakwai da aka haƙa a asibitoci.
Cikin waɗanda Isra'ila ta kashi, yara ne kashi 42, mata kashi 27 sannan maza kashi 31.
Yara ne suka fi shan wahala a wannan yaƙi, inda jarirai sabbin haihuwa 171 suka mutu jim ƙadan bayan zuwa duniya sannan yara 'yan ƙasa da shekara daya guda 710 suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila. Isra'ila ba ta bar har da 'yan tayi ba inda aka riƙa ganinsu a ƙarƙashin ɓaraguzai. Yara kimanin 25,973 sun rasa duka iyayensu ko kuma ɗaya daga cikin iyayen.
2014 GMT —Isra'ila ta kai sabbin hare-hare ta sama a kudancin Beirut
Kafofin watsa labaran gwamnatin Lebanon sun bayar da rahotannin da ke cewa Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a kudancin Beirut jim kaɗan bayan wa'adin da sojojin Isra'ila suka bai wa mazauna yankunan domin barin wuraren ya cika — inda suke ta yin luguden wuta.
"Jiragen yaƙin abokan gaba sun ƙaddamar da hare-hare biyu a yankunan da ke bayan garin kudancin Beirut, da farko sun kai hari a yankin Saint Therese, daga bisani suka kai hari a yankin Burj al-Barajneh," a cewar kamfanin dillancin labaran Lebanon National News Agency .
0307 GMT — An kashe sojin Isra'ila ɗaya a ba-ta-kashi a arewacin Isra'ila, in ji rundunar sojin ƙasar
Rundunar sojojin Isra'ila ta fitar da sanarwa da sanyin safiyar Litinin da ke cewa an kashe sojanta ɗaya yayin ba-ta-kashi a kan iyakar Lebanon sannan an jikkata sojoji biyu.
2036 GMT — An ɗage dakatarwar da aka yi ta tashin jiragen sama a Iran
An ɗage matakin da hukumomin Iran suka ɗauka na dakatar da tashin jiragen sama domin tabbatar da tsaron lafiyarsu, a cewar kafofin watsa labaran gwamnati, kamar yadda hukumar kula da sufurin jiragen sama ta sanar tun da farko.
1923 GMT — Hezbollah ta ce ta kai hari kan wani taron sojojin Isra'ila a yankunan da ke arewa
Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ci gaba da yin luguden wuta a yankunan sojoji da kuma wani taro na sojojin Isra'ila a matsugunan da ke arewaci inda ta yi amfani da jirage mara matuƙa da rkoki wajen kai hare-haren.
A wasu saƙonni da ta wallafa a shafin Telegram, ƙungiyar ta ce mayaƙanta sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da jirage marasa matuƙa a bataliyar soji mai lamba 7200 da kuma sansanin sojoji da ke kudancin Haifa, inda ta samu "wuraren da aka nufa kai-tsaye".
Kazalika Hezbollah ta ce mayaƙanta sun yi luguden wuta a kan wani taro sojojin Isra'ila a matsugunin Ma'alot Tarshiha "da rokoki da dama".