Wani mutum a ƙasar Indiya ya tashi ana dab da ƙona gawarsa.
Hukumomi a ƙasar sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne bayan sakaci da likita ya yi inda ya tsallake binciken da ake yi idan mutum ya mutu na gano musababbin mutuwarsa.
Rohitash Kumar mai shekara 25 wanda ke da matsalar ji da kuma magana, ya yi fama da rashin lafiya inda aka kai shi wani asibiti a Jhunjhunu da ke yammacin Jihar Rajasthan a ranar Alhamis.
Kafofin watsa labarai na Indiya sun ruwaito cewa mutumin yana fama da farfaɗiya inda likita ya ce ya mutu bayan kai shi asibiti.
A maimakon a yi bincike domin gano musabbanin abin da ya kashe shi, sai likitoci suka aika da shi matuware domin ajiyar gawarsa a cikin firji kafin ƙona ta kamar yadda addinin Hindu ya tanada.
D. Singh, wanda shi ne shugaban likitoci na asibitin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wani likita “ya shirya rahoto na binciken gawa ba tare da gudanar da ainahin binciken ba, inda daga bisani aka aika da gawar wurin ƙonawa”.
Singh ya bayyana cewa “ana dab da cinna wa gawar wuta, sai jikin Rohitash ya soma motsi”, inda ya ƙara da cewa “yana raye yana kuma numfashi”.
Nan take aka aika da Mista Kumar ɗin asibiti a karo na biyu, amma daga baya ya rasu a lokacin da ake ƙoƙarin yi masa magani.
Tuni hukumomi suka dakatar da ayyukan likitoci uku haka kuma ‘yan sanda sun ƙaddamar da bincike game da lamarin.