Ana iya ganin tartsatsain wuta a unguwannin kudancin Beirut, bayan hare-haren Isra'ila, kamar yadda ake iya ganowa daga Baabda / Hoto: Reuters

Asabar, 23 ga Nuwamba, 2024

0300 GMT — Isra'ila ta harba makamai masu linzami guda huɗu tsakiyar birnin Beirut na Lebanon, inda ta kashe aƙalla mutane huɗu da jikkata wasu 33, kamar yadda kafofin watsa labarai na ƙasar suka rawaito, inda suka ƙara da cewa ana fargabar adadin zai iya zarta haka.

An kai hare-haren ne unguwar Basta, a cewar mazauna yankin, suna masu ƙarawa da cewa an rusa gine-gine da dama.

Kamfanin dillacin labarai na gwamnatin Lebanon, National News Agency ya ce, jiragen yaƙin Isra'ila "sun ruguza wani gida mai hawa takwas baki ɗaya da makamai masu linzami biyar."

An riƙa jin jiniya a lokacin da motocin ɗaukar marasa lafiya ke rige-rige zuwa wajen da aka kai harin a unguwar Basta ta birnin Beirut.

Wani bidiyo da gidan talabijin na Lebanon Al Jadeed ya wallafa ya nuna aƙalla ɗaya daga gine-ginen da kuma lalata wasu gine-ginen da suke kusa da shi.

Hare-haren, waɗanda aka kai su da misalin karfe 4 na safe, ya zo ne kwana ɗaya bayan wasu munanan hare-hare a wata unguwa ta kudancin Birnin Beirut da kuma kudancin birnin Trye dake gaɓar ruwa.

TRT World