Isra'ila na ci gaba da kai hari a Gaza da Lebanon a kullum inda take kashe mutane da dama waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: Reuters

Lahadi, 24 ga Nuwamba, 2024

1154 GMT Isra’ila ta kashe sojan Lebanon da jikkata mutum 18 a wani hari ta sama da ta kai wani sansanin sojin Lebanon, kamar yadda sojojin suka sanar a ranar Lahadi.

Wata sanarwa da sojojin suka fitar ta bayyana cewa harin ya faɗa kan cibiyar soji da ke al-Amiriya da ke kan titin Al-Qalila-Tyre.

Sanarwar ta ƙara da cewa harin ya yi matuƙar ɓarna ga sansanin sojin.

Isra'ila ta fara yaƙi da kasar Lebanon, inda ta kaddamar da wani farmaki ta sama a karshen watan na Satumba, kan abin da ta ce tana kai wa kungiyar Hezbollah hari.

2122 GMT — An tilasta wa ɗaruruwan Falasɗinawa ficewa daga unguwar Shujaiya a birnin Gaza, bayan sabon umarnin fita da Isra'ila ta yi da barazanar jefa bama-bamai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai naWafa ya rawaito.

Iyalai da dama sun gudu daga yankin a ƙafa, inda suka bar gidajensu suna ɗauke da 'yan kayayyakin da za su iya, da abin rufa, kamar yadda Wafa ta faɗa tana rawaito majiyoyin yankin.

Mutanen da suka bar gidajen na su sun tafi zuwa kudanci da tsakiyar birnin Gaza don tsira da ransu.

0225 GMT — An kashe wani mutum bayan musayar wuta a yankin da ofishin jakadancin Isra'ila yake a Jordan: Kafar watsa labarai ta gwamnati

An harbe wani mutum an kuma jikkata jami'an tsaro uku bayan musayar wuta a wata unguwa a babban birnin Jordan inda ofishin jakadancin Isra'ila yake, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Petra ya rawaito.

"Hukumar Kula da Tsaro ta sanar da cewa ta fuskanci matsalar musayar wuta a wajen, yayin da jami'ai ke sintiri a yankin Rabieh a babban birnin ƙasar nan, Amman, da sanyin safiyar Lahadi," a cewar kamfanin dillancin labaran, yana mai ƙarawa da cewa, lamarin ya janyo "kashe mutumin da ya kai harin".

2009 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Lebanon ya kai 3,670

Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla ƙarin mutum 25 a faɗin Lebanon a kwanaki uku da suka gabata, abin da ya kai jumullar mutanen da aka kashe tun daga Oktoban bara zuwa 3,670, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon.

A wata sanarwa, ma'aikatar ta ƙara da cewa an kuma jikkata wasu mutane 58, abin da ya kai adadin waɗanda aka jikkata zuwa 15,413 tun daga Oktoban 2023.

Ƙarin labarai👇

2208 GMT — Jiragen Isra'ila marasa matuƙi sun kashe ma'aikatan lafiya biyu, sun jikkata 4 a yankin Tyre na kudancin Lebanon

Jiragen Isra'ila marasa matuƙa sun bi ma'aikatan lafiya a yankin Tyre na kudancin Lebanon, inda suka kashe biyu suka kuma jikkata huɗu daga cikinsu.

“Wani jirgin Isra'ila mara matuƙi ya nufi tawagarmu mai aikin ceto yayin da suke tafiya garin Ain Baal a gundumar Tyre don aikin ceto na gaggawa," kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta bayyana.

"Yayin da tawagar ceto to biyu ta tafi wajen da sauri don ceto waɗanda aka jikkata a tawagar farko, ita ma jirgin Isra'ila mara matuki ya kai mata hari, abin da ya janyo shahadar mutum biyu da jikkata mutane huɗu daga tawagogin biyu."

2139 GMT — Hare-haren Isra'ila ta sama sun kashe mutum 20 a tsakiyar Beirut

Adadin mutanen da suka mutu a harin jiragen yaƙi da Isra'ila ta kai tsakiyar Beirut ya kai 20, yayin da aka jikkata wasu 66, a cewar Ma'aikatar Lafiya.

Kamfanin dillancin labarai na gwamnati na Lebanese National News Agency ya ce harin ya rusa wani gida mai hawa takwas a titin Al-Mamoun a gundumar Basta.

Tawagar masu aikin ceto da masu ba da agajin gaggawa suna aiki domin zaƙulo mutane daga ɓaraguzai da kuma taimakon waɗanda suke da sauran numfashi. An gaggauta tafiya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci, wasunsu suna cikin mawuyacin hali.

TRT World